Ya Fake da Sunan Jiga-jigan Shehunan Tijjaniyya Yana Damfarar Al’umma Kudade.

Ya Fake da Sunan Jiga-jigan Shehunan Darikar Tijjaniyya Yana Damfarar Al’umma Kudade.

 

Daga Manzo Mustapha Khalifa

 

Wannan bawan Allah da kuke gani yana faɗiwa mutane cewa; Shi Jikan Shehu Gibrima (RTA) ne, Kullum bashi da aiki sai zuwa garuruwa da ƙasashe maban-banta wurin Damfarar mutane da yin zinace-zinace da luwaɗi da cutar mutane. Wal’iyazu Billah.

 

Kuma duk lokacin da aka jiyo labarin cewa; wani yayi abun kunya da sunan Jikan Shehu gibrima (RTA) to cikin Ɗari Saba’in duka shine don haka muna masu nusar da mutane cewa; wannan ba Jikan Shehu bane Kwata-kwata bashi da alaƙa da su.

 

Bugu da Kari yanzu haka ya damfari mutane a Kotono kuma ya nufi ƙasar Ghana, Muna kira da mutane duk wani wanda yake da kusanci da wasu ƴan uwa da suke Ghana yayi ƙoƙarin sanar dasu wannan al’amari gudun kada da nasani yabiyo baya.

 

Kuma da akwai wasu da suke aikta irin aikinsa na faɗin cewa su jikokin Shehu ne wadanda muna gari ɗaya dasu kuma man sansu, suna yaudarar mutanen Ƙasar Libya. Muna jan kunnen su su daina idan ba haka ba zamu ɗaura hoton ku da muryar ku. Idan kunne yaji.

 

Ga duk wanda ya samu labarin sa to da Allah yakira waɗannan layi kan.

 

07032123940. +2348141505312

+2347016669979. 08030686899.

Share

Back to top button