Sheikh Prof Ibrahim Maqari Ya Gabatar Da Mauludin Manzon Allah SAW A Birnin Zaria

Farfesa Ibrahim Ahmad Makari Ya Jagoranci Gabatar Da Maulidin Manzon Allah SAW A Zariya.

 

Daga Akeel Abdulkadir (Abu Muslim)

 

A Daren Daya Gabata Talata , 25 Ga Watan oktoba 2022 Limamin Babban Masallacin Kasa Dake Abuja Parfesa Ibrahim Makari Yajagoranci Gagarimin Taron Maulidin Manzo Allah ( S A W) A Haraban Babban Masallacin Juma’a Dake Kofar Fadan Zazzau A Zariya.

 

Taron Maulidin Yatara Mashuran Mutane Naciki Da Wajen Zariya , Tundaga Malaman Addini Daliban Ilmi Sarakuna Shuwagabanin Al umma , ‘Yan kasuwa yan Siyasa Dasauransu..

 

Sheikh Umara Bn Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini Shine Babban Bako Malami Daya Fara Jawabi , Hakanan Malamai Daga Kano Zamfara Abuja Dasauran Garuruwa Sungabatar Da Jawabi Awurin .

 

Babban Limamin Zazzau Sheikh Dalhat Kasim Imam Shine Ya Wakilci Mai Martaba Sarkin Zazzau Amb. Ahmad Nuhu Bamalli Tare da Rakiyar Wasu Hakimai.

 

Ankwashe Tsawan Dare Zuwa Wayewar Gari Ana Gabatarwa , Bayaga Jawabai Na Munasaba Maulidin Hafizan Sunyita Karaun Al Qur’ani Mai Girma , Hakama Karatun Diwani.

 

An Gabatar Da Maulidin Ne Karkashin Zawiyyar Sheikh Sharif Saleh Alhusaini Dake Zariya , Taron Yatara Dunbin Al umma Kuma Ya Kayatar Kwarai Dagaske.

Back to top button