MUSAN ADDININ MU: AZABAR WANDA BAYA WANKAN JANABA.

AZABAR WANDA BAYA WANKAN JANABA

 

Kafin inyi bayani akan azaba ga wanda baya wankan janaba, bari mu fara sanin TSARKI DA ABINDA YA QUNSA.

 

Tsarki kalmar hausa ne dake nufin tsabta, ya kuma samo asali ne daga kalmar larabci (الطهارة). A musulunci, ana tsarki ne da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa. Wato ruwan da bai canja dandado, qamshi ko kalar sa ba ta hanyar haduwa da wani abu. Amma misali ruwan rijiya mai kanwa ko ruwan teku ko ruwan rafi, ba su da matsala tunda canjin dandado ko launin su daga Allah ne ba mutum ne yayi ba.

 

Tsarki ya rabu kashi biyu kamar haka:

 

1. HADASI: Shine najasar da kan sami mutum ta kofofi guda biyu wato DUBURA ko kuma AZZAKARI/FARJI. Ana gusar da wayannan najasar ne ta hanyar tsarki ko wanka. Najasar hadasi sun hada da:

A. Fitsari

B. Kãshi

C. Fitar maniyyi

D. Yankewar jinin haila ko nifasi

E. Shigar kafuri musulunci

 

Fitsari da kashi ga mace ko namiji, tsarki kawai ake yi, ba a buqatar wanka, sune kuma ake kira HADASUL AS-GAR. Amma abubuwan dake wajabta wanka sune HADASUL AKBAR, kamar shigar azzakarin namiji cikin farjin mace koda bai fitar da maniyyi ba, fitar maniyyi daga namiji ko mace ta hanyar jima’i ko masturbation (istimna’i) ko mafarki, in kafuri ya shiga musulunci, sai kuma yankewar jinin haila ko biqi.

 

2. KHABASI: Ya qunshi najasar da kan shafi jikin mutum, tufafin sa da wurin ibadar sa. Akwai najasar da basu da aibu, kamar majina da ruwan qurji. Amma ruwan gutter, fitsari a jiki ko ya fantsama a kaya, jini da sauran su, suna najastar da jikin mutum mai ibada ko tufafin sa ko inda zai yi ibadar, har sai ya wanke su da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa.

 

Nana Aisha RTA ta bada labarin yadda Annabi SAW yake wankan janaba, gashi misalin sa kamar haka:

 

Ana samun kwarya (bokiti a zamanin mu ko buta) cike da ruwa mai dumi kuma mai tsarki mai tsarkakewa, a wanke hannaye sau uku kafin a tsoma su cikin kwaryar, amma in buta ne ba sai an wanke hannayen ba. Sai ayi niyyar wankan janaba wato ALLAHUMMA INNI NAIWAITU HAZAL GUSLI LIR-RAF’IL HADASIL AS-GAR WAL AKBAR. Sannan a wanke tsakanin cinyoyi da azzakari/farji sosai gwargwadon inda ake tunanin najasar zata iya shafa, sai ayi alwalla tun daga hannu zuwa shafar kunne amma sau daya-daya za a wanke ko ina, sannan a wanke kai dukkan sa da wuya da fuska sau uku, sannan a wanke sashin jiki na dama daga sama har qasa, sannan a sake yin haka ga sashin hagu, sannan a matsa gefe kadan a wanke kafafu. Shikenan anyi wankan janaba.

 

Amma an yarda mutum yayi niyya ya fada rafi ko ya kunna shower ko ya daga bokiti ya game ko ina a jikin sa da ruwa, wankar sa tayi, saidai wancan na farin shine cikakken wanka wanda Annabi SAW yake yi, mu ma shi muke yi.

 

Duk wanda wanka ya wajaba akan sa amma yaqi yi, alwallar sa ba zata karbu ba ballantana salla, idan kuwa ya mutu da wannan najasar, azabar sa shine za a dinga sarar jikin sa da gatarin jahannama ana kankare najasar kamar yadda ake sarar jikin itace don cire bawon ta.

 

Waliyai suna cewa, ba ma zama da mutumin da janaba zata kama shi amma yayi jinkirin yin wanka na tsawon minti biyar, ba fa awa daya ba ballantana wanda zai iya wuni ko sati bai yi ba.

 

Komi tsadar sabulun da kake wanka dashi, Rashin wankan janaba yana haifar da warin qashi, yana gayyato aljanu zuwa jikin mutum, yana nisanta mutum da mala’ikun rahma, yana sanya kasala da cututtuka a jiki.

 

INA KIRA GA YAN’UWANA AKAN MU NEMI ILIMI DOMIN MU INGANTA IBADAR MU, KO DAI MU KOMA MAKARANTA A ZAHIRI KO MU KULLA ABOTA DA WANI MALAMI WANDA ZAI DINGA KOYAR DAMU ILIMI KODA TA WAYA NE KO VIDEO CALL, KO MU DINGA BINCIKE A YOUTUBE A SHAFUKAN ADDINI.

 

Daga: Sidi Sadauki

Share

Back to top button