A fa Nusar da Sarkin Kano da Kyau, Tabbas Da Muguwar Rawa Gwara Ƙin Tashi. Daga Dr, Shehi Mai Jama’a
A fa Nusar da Sarkin Kano da kyau !
Tabbas Da Muguwar Rawa Gwara Ƙin Tashi…
Jawabin da Sarkin Kano Khalifa Sanusi Yayi, Sam Sam bai da Fa’ida, Kuma Rashin yin sa ya fi Alheri, ba kuma zai Haifar masa da Komai ba sai Ƙara Lalata Al’amura.
Kuma Ina masa Fatan samun Mashawartan da za su Ringa Nusar da shi akan “MAGANA” da ya Kamata ya dinga yi, da kuma lokacin da ya kamata yayi shiru.
Alaƙa Tsakanin mu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam (Musamman mu Sufaye) Alaƙa ce ta Ladabi Tsantsa Kawai, kuma ko da Wane Nassi Ladabin nan ya ci Karo; to muna Jefar da Nassin ne, mu Gabatar da Ladabi, har ma Muna da Ƙa’idar nan ta ( الأدب أولى من الامتثال )
Magana fa Ake Akan Haruffan da ke Ɗauke da Sunan ( MUHAMMADU ), Wanda mu ba batun za a Iya Takawa muke ba, A’a !! Mu Muna batu ne na cewa Rubuta su ma Kaɗai a Dandaɓaryar Ƙasa, Gundumemen Laifi ne da da ba zai taɓa Karɓuwa ba a zukatan mu.
وتحسبونه هينا وهو عند الله عظيم