A Karanta ‘Suratul Fil’ Kafa Milyan Daya Da Dubu Dari Daya Da Sha Daya (1,100,111) Domin Samun Waraka Daga Matsalolin Nijeriya, Sakon Sheikh Dahiru Bauchi Ga Musulman Nijeriya.

A Karanta ‘Suratul Fil’ Kafa Milyan Daya Da Dubu Dari Daya Da Sha Daya (1,100,111) Domin Samun Waraka Daga Matsalolin Nijeriya, Sakon Sheikh Dahiru Bauchi Ga Musulman Nijeriya

 

Shugaban kungiyar malaman alkaluma (UHAN) Mal. Habibi Abdallah Assufiyu ya bayyana cewa” Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bada tabarrakin addua’a da za’ayiwa kasar nan.

 

Assufiyu yayi kira da cewa “Muna masu Sanar da membobin kungiya a duk fadin kasa, kuma a kowacce tsangaya da sauran al’umma Musulmi da a karanta suratul fil million daya da dubu dari daya da guda goma sha daya.(1,100,111) domin Allah ya tona asirin duk wanda keda hannu akan matsalar tsaro a kasar nan, tare da kawo karshen su.

 

Ya kara da cewa “Mun samu wannan tabarrakin addu’a daga babban shehin mu na Darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, bisa duba da yadda matsalolin ta’addanci ke kara ta’azzara a kasa. Shehu yayi Umurni da a yawaita istigfari da salatin Annabi ayayin gudanar da wa’annan addu’o’i namusamman.

 

A karkashin wannan Kungiya muna umurtar kowanne jagora na wannan kungiya daya tabbatar an cika wannan adadi da shehu ya bayar na suratul fili, a iya tsawon sati biyu zuwa wata daya.

 

Allah ya amsa mana ya kuma kawo karshen ta’addanci a Nigeria. Allah yazaba mana shugabanni Nagari. Amin.

Share

Back to top button