A Madadin Darikar Tijjaniyya Karkashin Jagoranci Fityanul Islam Initiative Ta Kasa Tana Mika Sakon Ta’aziyya.

GAISUWAN TA’AZIYYA

 

…..A madadin darikar Tijjaniyya karkashin kungiyar Fityanul Islam Initiative ta kasa tana mika sakon ta’aziyya ga daukacin al’umma.

 

A daren jiya lahadi ne 03/12/2023, wani abun bakin-ciki ya faru da yan’uwa Musulmai a yayin da suke gudanar da taron Mauludin Manzon Allah SAW rundunar sojojin saman najeriya suka harba masu Bom a garin Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna.

 

Wanna lamarin ya faru ne da misalin karfe 9pm na daren Lahadi a yankin dake kusa da Filin Jirgin Sama na Kaduna a arewacin Najeriya.

 

Wani mazaunain yankin ya ce “mutane na cikin bikin Mauludi kawai sai jirgin sama ya jefo masu bom wanda ya yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 a wurin, tare da jikkata mutane da dama” inji shi.

 

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ki bayyana yawan wayanda suka rasa rayukansu ba.

 

Amma ya ce za su sanar da manema labarai abin da ya faru a wurin bayan sun yi taron gaggawa na majalisar tsaron jihar.

 

Rundunar sojojin saman najeriya ta fito ta karyata wannan lamarin, inda tace basu ne suka aikata wannan harin Bom din ba, tare da nuna rashin masaniyar su akan harin Bom din.

 

Muna addu’an Allah ya jikan su da rahma ya gafarta masu, Allah ya tona asirin wadanda suka aikata wannan harin Bom. Amiiiin

Share

Back to top button