A Rana Mai Kamar Ta Yau 9 Ga Watan Safar Shekara 37 Bayan Hijira Ammar ibn Yasir Yayi Shahada.

Tarihin Ammar ibn Yasir. أبو اليقظان عمار ابن ياسر ابن عامر ابن مالك العنسي المذحجي) Wanda Yayi Shahada A Rana Mai Kamar Ta Yau 9 Ga Watan Safar Shekara 37 Bayan Hijira.

 

Abu ‘l-Yaqẓān ‘Ammār bn Yasir bn ‘Amir bn Malik al-Ansīy al-Maḏḏḥiǧī wanda kuma aka fi sani da Abūl Yaqẓān ‘Ammār bn Sumayya ya kasance ɗaya daga cikin Muhajirun da ya sadaukar da rayuwarsa a tarihin Musulunci, kuma ya sadaukar da rayuwarsa ga Musulunci. a matsayin daya daga cikin makusanta kuma mafi aminci ga sahabban Annabi Muhammadu sallallahu Alaihi wasallam da musulmi.

 

Dan kabilar Banu Makhzum ne, A Hizaj ( Saudi Arabia Ta Yanzu) An haifi Ammar bn Yasir ne tsakanin shekara ta 53 da ta 57 kafin hijirar Ma’aiki SAW, (567) Miladiyya, Mahaifinsa shi ne Yasir sannan mahaifiyarsa kuwa ita ce Sumayya wadanda suka yi shahada tun farko-farkon Musulunci sakamakon azabtarwar da kafirai suka yi musu saboda karbar kalmar Shahada.

 

Ammar ya musulunta a farkon musulunci bisa gayyatar Sayyadina Abubakar ( RA ) Ana kirga Ammar bn Yasir daga cikin musulman farko da suka fuskanci takurawa da azabtarwa daga mushirikan Makka, sannan kuma daga cikin musulman da suka yi hijira zuwa Madina. Ammar bn Yasir ya halacci yakukuwan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi irinsu Badar da Khandak, inda ya kashe wani adadi mai yawa na kafirai. Bayan Wafatin Ma’aiki, ya kasance daga cikin Sahabban da suka yi kira zuwa ga mubaya’a wa Amirul Muminina Ali bn Abi Talib ( RA) a matsayin halifan Ma’aiki, don haka yana daga cikin wadanda suka taru a gidan Fatima al-Zahra ( AS ) Ammar na daga cikin na kurkusan da suka yi wa Zahra sallah bayan rasuwarta da kuma bisne ta a boye.

 

Kamar yadda yana daga cikin mabiya Ali (AS ) na kurkusa wadanda suka mika masa dukkan rayuwarsu wajen kare shi da kuma tafarkin da yake kai. Ammar bn Yasir yana daga cikin ‘yan kalilan din da Allah da Manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallam da kuma Ahlulbaiti suka yi musu kyakkyawar shaida kan irin matsayin daraja da imani mai girma da suke da shi.

 

A cikin Alkur’ani mai girma Allah Ya yi masa shaida da cewa zuciyarsa cike take da imani, wato lokacin da kafiran Makka suka tilasta masa fadin wasu kalmomi na batanci ga Ma’aikin Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Musulunci bayan sun kashe mahaifansa (Yasir da Sumayyah), inda Allah Madaukaki Ya ke cewa: Sai dai wanda aka tilasta alhali zuciyarsa na cike da imani. (Suratun Nahl 16:106). A wannan lokacin ma an ruwaito Manzon Allah (SAW) yana cewa: Ya Ammar! Idan sun dawo (idan sun sake tilasta maka) to ka fadi (abin da ka fadi Ba a baya) don kuwa Allah Ya karbi uzurinka, kuma Yana umartanka da ka sake fadi (abin da ka fadi Ba) idan suka sake dawo maka”. Akwai maganganu daban-daban na Ma’aikin Allah (SAW) kan Ammar bn Yasir da suke nuni da daukakan matsayinsa duniya da lahira. Ga kadan daga cikinsu:

 

1, Ammar cike yake da imani tun daga kansa har zuwa kafarsa, kamar yadda imani ya hadu da nama da jininsa.

 

2, Jini da nama da kashin Ammar sun hatamta ga wuta.

 

3, Aljanna tana shaukinka (Ya Ali) da kuma Ammar, Salman, Abu Zar da Mikdad.

 

4, An ce lokacin da ake gina masallacin Annabi a Madina, Ammar ya kasance ya kan dauko duwatsu guda bibbiyu, ganin haka sai Manzon Allah ( SAW) ya shafa bayansa ya ce: ” Kai kana daga cikin ‘yan Aljanna, da fandararrun Yan kungiya za su kashe.

 

Bayan Wafatin Ma’aiki Sallallahu Alaihi wasallam Ammar ya kasance tare da Amirul Muminina (RA) har lokacin da jama’a suka zabe shi a matsayin halifa. Don haka ya yi yaki tare da Amirul Muminina (AS) lokacin halifancinsa har lokacin da ya yi shahada.

 

Irin gaskiya da imanin da yake da shi ya sanya Amirul Muminina (AS) ya ba shi rikon wasu mukamai da suka hada har da gwamnan garin Kufa, kwamandan yaki, jagorantar tube Abu Musa al-Ash’ari daga gwamnan Kufa. Sannan kuma daga cikin wadanda suka raka Abu Zar zuwa inda aka kore shi gudun hijira wato Rabaza.

 

Shahada a Yakin Siffin.

 

Shahadarsa Daya daga cikin rahamar Ubangiji Madaukakin Sarki ga bayin Sa na gargaru ita ce sama musu karshe mai kyau da kuma daukaka, wato arzurta su da shahada.

 

Ammar bn Yasir dai na daga cikin irin wadannan bayi da aka Azurta su da shahada sannan kuma aka samar da su tun ma kafin lokacinta. An ruwaito cewa a yakin Siffin, Ammar bn Yasir (RA) ya fito don fuskantar makiya, inda ya bukaci a ba shi ruwa ya sha, sai aka ce masa ai babu ruwa. Ganin haka sai wani daga cikin Ansarawa (mutanen Madina) ya kawo masa nono, ya sha sai ya ce: “Haka kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ke cewa karshen guzurina a duniya shi ne nono”. Daga nan sai ya fuskanci makiya, inda ya kashe mutane 18, ganin haka sai wasu mutane biyu daga cikin kungiyar makiya wato Ibn Jawn al-Sukuni da Abul Gadiya a al-Fazari suka far masa, al-Faraz ya soke shi da mashi shi kuma dayan ya sari kansa. Wannan lamari dai ya faru ne a watan Safar Shekaru 37 bayan hijira a lokacin kuma Ammar yana dan shekaru 90 a duniya. Ta haka ne Ammar bn Yasir ya yi shahada da samun wannan madaukakin matsayi.

 

Musulmai suna ganin kashe Ammar a matsayin abin da ba a taba ganin irinsa ba a cikin makomar sahabban Annabi ( SAW) domin suna ganin mutuwarsa a yakin Siffin a matsayin yanke hukunci tsakanin kungiyar salihai da masu zunubi a Fitina.

 

Ammar bn Yasir ya kasance ɗaya daga cikin manyan Sahabban Manzon Allah (SAW) masu daraja , wanda Annabi yayi masa bushara da cewa rundunar Azzalumai ce za ta kashe shi , kuma hakan ta faru bayan shekaru masu yawa da komawar Annabi ga Ubangijinsa , inda Ammar Ben Yasir yayi shahada a hannun rundunar Azzaluman Sham (Rundunar Mu’awiyah ɗan Abi Sufyan ) . Shahadar Ammar Bin Yasir tana daga cikin Mu’ujizozin da Annabi ya bada labarinsu , kuma tana tabbatar da kasancewar rundunar Sarkin Sham Mu’awiyah a matsayin ƴan Azzaluman ƴan Ta’adda.

 

Khuzaimatu bin Thabit Al-ansari , wanda ake ma laƙabi da Zush shadataini (ma’abocin sheda biyu ) , shima yana daga cikin manyan Sahabbai, da suka Sallamawa Annabi da iyalan gidansa , kuma suka tsaya tsayin daka a bayan Annabi (SAW) wajen kare iyalansa, tun daga Saƙifa har ranar da yayi shahada a tare da Imam Ali (AS) Kuma ya kasance mawaƙi da ya yawaita yabon Imam Ali da bayanin matsayinsa da falalarsa .

 

Shima Hashim bn Utbatu bn Abi Waƙkas, wanda aka fi sani da (Almirƙal) , yana daga cikin Sahabban da suka bawa Musulunci gudummawa kuma ya kasance cikin rundunar Imam Ali (RA) a yaƙin Siffin, a lokacin da Alharis Bn Munzir ya lallaɓo ya sokeshi a cikinsa , hakan yayi sanadiyar shahadarsa .

 

KARIN HASKE.

 

An haife shi ne a shekarar giwaye wato shekarar da aka haifi Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, a Makka kuma yana daya daga cikin masu shiga tsakani a Auren Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama da Khadijah bint Khuwaylid . Mahaifinsa Yasir bn Amir dan kabilar Qahtan ne a kasar Yaman ya yi hijira zuwa Makka ya zauna a can bayan ya auri Sumayyah bint Khayyat , kuyanga; Ammar da iyayensa Yasir da Sumayya bayi ne ga Abu Huzaifa, amma bayan rasuwarsa, Abu Jahal .-wanda daga baya ya zama daya daga cikin manya-manyan makiyan Musulunci kuma wanda ya yi kaurin suna wajen azabtar da Ammar da iyayensa- ya karbe su a matsayin bayinsa. Amincewar Ammar da sanin amincin Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama tun kafin Annabcinsa, sun ƙarfafa shi ya bi Bayan wahayin annabcin Annabi SAW matsayin ɗaya daga cikin farkon masu tuba.

 

Share

Back to top button