A Tashi Tsaye Da Addu’o’i A Masallatan Juma’a ..Inji Sheikh Kabir Yusuf Shugaban Fityanul Islam Initiative

Kungiyar Fityanul Islam Initiative Ta Kasa Ta Shawarci Limaman Juma’a Da Suyi Addu’o’in Na Musamman Kan Kisan Musulmai Masu Mauludi A Garin Tudun-Biri Dake Jihar Kaduna.

 

Daga: Babangida Alhaji Maina.

 

Shugaban sabuwar kungiyar Fityanul Islam Initiative ta kasa Sheikh Farfesa Muhammad Kabir Yusuf Hamdani ya shawarci daukaci limaman juma’a da su gudanar da addu’o’in na musamman a yayi gabatar da Kudbah a nasallatai kan kisan yan’uwa masoya Annabi Muhammadu SAW a gurin taron Mauludin Manzon Allah SAW a kauyen Tudun-Biri dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna.

 

Farfesa Muhammad Kabir Yusuf ya wannan kiran ne don nunawa duniya irin zaluncin da aka aikata na kisan bayin Allah (SWT) wanda basu ji basu gani ba. Ya bayyana takaicin sa na faruwan wanna al’alamari wanda wannan ba shine na farko da hakan yake faruwa a arewacin Najeriya ba na kissn gangaci.

 

Bayan Haka; Farfesa Kabir Yusuf yayi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da ta dauki matakin gaggawa don zakulo wanda suka aikata wannan mummunan hari kan masu Mauludi tare da tabbatar da an bi masu kadun su. Tare da gudanar da bincike don kaucewa faruwan haka a nan gaba.

 

A karshe ya kara mika sakon ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmai duniya musamman masoya Annabi Muhammadu SAW da kuma iyalan wanda Allah ya karbi shahadar su.

 

Allah ya jikan su da rahma ya gafarta masu, Allah ya karbi bakwancin su, wadanda suke kwance Allah ya basu lafiya ya kare dukkan al’ummar musulmai baki daya, ya tona asirin wadanda suke aikata wannan hari. Amiin

Share

Back to top button