A Yau, Duk Wanda Ya Kalli Karatu/wa’azi a TV Ko Yaji a Radio To Sheikh Ibrahim INYASS Yana Da Ladan Hakan

DUK FADIN DUNIYA SHEIKH IBRAHIM INYASS RA SHI YAYI DALILIN FARA SANYA KARATU A KAFAFEN SADARWA.

 

A shekarar 1960 Yahudawa sun tashi sun bazama wurin bata Alqur’ani ta kowace fuska. Wannan al’amari ya tada hankalin musulman Duniya sun rasa yadda za su yi, Kwatsam sai aka tara malaman duniya a kungiyar hadin kan malaman Duniya na musulunci a kasar Saudiyya

الرابطة العالم الإسلامي

 

Domin a nemo mafita

 

A lokacin sai akayi sa’a SHEIKHUL ISLAM ( SHEIKH IBRAHIM INYASS ) ya halarci wannan taro. Ganin matsalar yadda take sai ya rubuta wannan littafi Mai suna:

 

الحجة البالغة في كون إذاعة القرآن سائغة

 

“GAMSASSHIYAR HUJJA AKAN CEWA ALQUR’ANI ANA IYA RERA SHI A TV KO RADIO”

 

Wannan littafin ya kosar da Duniyar Musulunci daga ishin ruwa da ya dameta; domin a lokacin Mafi yawan manyan maluman musulunci suna ganin haramun ne a Sanya wa’azi a kafafen sadarwa ( TV, radio, etc )

 

Dalilin wannan littafin ne a ka gamsu, aka samu damar yin Tafsirai da wa’azi acikin Radio da TV

 

Shugaban kasar Misra Jamal Abdulnasir tare da Sheikhul Islam ( Sheikh Ibrahim Nyass ) ne suka tsara yadda Khalil Khusri zai yi Audio kuma a dinga sashi safe da yamma a Media

 

A yau, duk Wanda ya Kalli karatu/wa’azi a TV ko yaji a Radio to Sheikh Ibrahim INYASS yana da ladan hakan, saboda fadin ANNABI S.A.W :

 

من سن سنة حسنة فله أجرها وأجر من عمل بها إلئ يوم القيامة

 

“Duk Wanda ya assasa Wani hanya Mai kyau, yana da ladan hakan, da ladan duk Wanda yayi amfani da wannan hanya, har tashin qiyama”

 

Allah ya saaka wa SHEIKHUL ISLAM ya kara masa kusanci da ANNABI MUHAMMAD

 

صلى الله عليه واله وسلم Ameen!

 

ALIYU ABDURRAHMAN

Share

Back to top button