ABIN ALFAHARI: Wasu Daga Cikin Matasan Tijjaniyya Sun Wakilci Najeriya A Musabaqar Alkur’ani Na Duniya.

Matasan Tijjaniyya Sun Wakilci Najeriya A Musabaqar Alkur’ani Na Duniya A Kasar Saudiyya.

 

Daya daga cikin matasan da suka wakilci Najeriya a gasar musabakar Al-Qur’ani ta Duniya a karo na 43, Alaramma Abdullahi Sadiq yau yahau mimbari, ya rera karatun Al-Qur’ani mai Girma, mai dadin ji da dadin sauraro.

 

A gobe Talata, shima Alaramma Muntaqa Ishaq, zai hau mimbari. Duka matasan guda biyu ‘yan asalin jihar Zamfara ne dake kasar Najeriya.

 

Muna musu fatan alkhairi a gare su baki daya. Allah ya basu nasara ya taimake su. Amiin

 

Daga: Comr Abba Sani Pantami

Share

Back to top button