ABIN ALFAHARI: Yar Shekara 13 a garin Kagara Jihar Katsina ta rubuta Alkur’ani Mai girma.

‘Yar Shekara 13 a garin Kagara Jihar Katsina ta rubuta Al-Qur’ani Mai girma cikakke

 

Daga Ibrahim Adamu Kagara

 

Wakilin ALFIJIR HAUSA Ibrahim Adamu Kagara ya hallarra wannan taro a domin tattaro maku duk Abubuwan da ke faruwa a wurin, na Wata yarinya ‘yar shekara 13 mai suna Zuwaira Ahmed da ke kauyen Kagara a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ta haddace tare da rubuta cikakken Hizfi (Babi) na Alkur’ani Mai Girma daga tunawa da ita.

 

Da yake jawabi a wajen bikin karrama yarinyar a ranar Asabar, Hakimin Mahuta, Alhaji Bello Abdulkadir, ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba.

 

Ya bayyana cewa; wannan babbar nasara ce da al’umma, da ma jihar baki daya, musamman a bangaren ilimin addinin Musulunci.

 

Abdulkadir ya ci gaba da yabawa iyaye a yankin, malamai da sauran shugabannin al’umma kan yadda suke kula da tarbiyyar ‘ya’yansu yadda ya kamata, yana mai kira gare su da su ci gaba da yin hakan.

 

Danejin Katsina ya baiwa sarakunan jihar tabbacin cigaba da bada goyon baya ga duk wani abu da ya shafi addinin musulunci domin cigaban yankin baki daya.

 

Shugaban Majalisar Kafur, Alhaji Garba Abdullahi-Kanya, ya yaba da kwazon yarinyar tare da ba da tabbacin tallafa mata a matakin Sakandare da Sakandare.

 

ALFIJIR HAUSA ta tattaro maku cewa; Shugaban makarantar ta na Madrasatul Tahfiz, Sheikh Sani Kagara, ya ce an kafa makarantar ne da nufin yin tasiri na ingantaccen ilimin addinin Musulunci a tsakanin matasa a cikin al’umma.

 

A cewarsa na wurin Cigaba da Zantawa da Wakilanm, yarinyar ta haddace Alkur’ani ne a cikin shekaru hudu, kuma ya danganta nasarar da suka samu ga goyon bayan iyayenta da jajircewar malamanta a makaranta.

 

A nasa jawabin, mahaifin Zuwaira, Malam Ahmed Sani, ya yaba da irin tallafin da aka ba shi da ‘yarsa, inda ya yi kira ga iyaye da su bar ‘ya’yansu su samu ilimin addinin musulunci da na kasashen yamma.

 

Ya kuma ba da tabbacin ci gaba da ba ta goyon bayan da ya dace don kuma ta ci gaba da karatun ta na yamma, inda ya ce a halin yanzu tana makarantar firamare a yankin.

Share

Back to top button