AKWAI DARASI MAI TARIN YAWA WAJEN KYAUTATA ZATO GA ALLAH SWT.

A KARANTA DA KYAU DOMIN AKWAI DARASI MAI TARIN YAWA WAJEN KYAUTATA ZATO GA ALLAH UBANGIJIN RAHMA:

 

Wata mata ta je gurin Annabi Dauda (AS) cikin fushi, ta ce masa: “Ya Annabi Allah! Ubangijinka yana da adalci kuwa?

 

Sai ya ce: “Kwarai kuwa, mai adalci ne, ba ya zalunci.

 

Menene labarin ki?

 

Sai ta ce: “Ni bazawara ce, ba ni da mai taimaka min, ga ‘ya’ya mata guda 3 marayu. Ina ciyar da su ne da sana’anar saka da nake yi.

 

Jiya na yi sakata mai yawa, na daure a wani jan tsumma, zan tafi kasuwa na sayar, na sami abin da zanciyar da kaina da ‘ya’yana, sai wani tsuntsu ya zo ya wafce daga hannuna. Kuma ba ni da komai, ga marayu.

 

Kafin Annabi Dauda (AS) ya ce komai ga wannan mata, sai ga wasu mutane su 10 sun shigo, kowannen su da Dinare 100 a hannunsa, suka ce:

 

“Ya Annabi Allah! Muna son za mu yi sadaka da wannan kudi..

 

Sai Annabi Dauda (AS) ya ce da su: “Me ya faru?” Sai suka ce: “Muna cikin jirgin ruwa, sai iska mai karfi ta taso, jirgin namu ya bule, sai muka dinga ambaton Allah, kuma muka yi bakancen idan Allah Ya tseratar da mu, za mu yi sadaka da Dinare dari-dari.

 

Muna cikin wannan hali, sai wani tsuntsu ya jeho mana wani jan tsumma, a cikin tsumman akwai wata saka.

 

Sai muka toshe bular da wannan sakar, Allah Ya tseratar da mu.

 

Sai Annabi Dauda (AS) ya yi godiya ga Allah, ya fuskanci wannan mata ya ce mata: “Ubangijinki mai adalci ne.

 

Idan kin yi sakar nawa kike siyarwa?”

 

Sai ta ce: “Dirhami daya”.

 

Sai ya ce: “Ga Dinare 1000, Allah Ya sayi sakarki, karbi ki je ki ciyar da ‘ya’yanki”.

 

Allahu Akbar

 

Allah yasa mudace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W). Amiiiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button