Alakar Darikar Tijjaniyya Da Darikar Kadiriyya A Addinin Musulunci.

ALAKAR MU DA YAN QADIRIYYA

 

Dariqar Qadiriyya itace dariqar Sidi Abdulqadir Jilani al-Baghdadi Radiyallahu Ta’ala Anhu. Cikakken Sharifi, babban waliyi Qudubi, wanda ya fara bayyana karamar sa tun a tsummar goyo, shehin da har shehin mu Qudubul Maktum Shehu Ahmadu Tijjani Radiyallahu Ta’ala Anhu yayi dariqar sa.

 

In ba don lallai Shehu Tijjani zabin Allah bane, toh da har tashin duniya, ba za ayi waliyyi kamar Sidi Abdulqadir ba, ba za a samu dariqa sama da tasa ba.

 

Amma abinda ya faru shine, kamar yadda Annabi SAW yake tun azal shugaba kuma cikamakin Annabawa da manzanni, Haka Shehu Tijjani RTA yake shugaba kuma cikamakin waliyan farko da na Qarshe. Kamar yadda Annabi SAW yake bautawa Allah ta sigar Ibadar Manzanni magabata har zuwa lokacin da aka yi isra’i da mi’iraji dashi ya karbo tasa sallar, haka Shehu Tijjani RTA yayi sufancin sa bisa tsarin dariqun sauran waliyai magabata kafin ranar da Annabi SAW ya bayyana garesa yayi masa umurnin ajiye su da riqo da TIJJANIYA kawai.

 

Na zauna da wani batijjanen sufi a kano, Sidi Muhammadul Kabir, nake tambayar sa sha’anin Sidi Abdulqadir da Shehu Tijjani, yace Ai Imam Hassan ne Shehu Tijjani, Imamu Hussaini ne Sidi Abdulqadir. Abin nufi, ruhukan su ne a jikin wayannan waliyai.

 

Tabbas muqamin Shehu Tijjani ya daukaka akan duk wani waliyyi banda sahabbai da Annabawa, za ka fahimci haka ne in ka samu ingantacciyar kissar haduwar Shehu Umarul Futi (Batijjane) da Shehu Usman Dan Fodio (Baqadire).

 

FADAR QADAMAYA HATANI

FA ILLA ANTA TIJJANI

ABIN FA NUFA GA JILANI

MUTANEN NASA ZAMANI

FA KAI KO KULLU AZMANI

 

A DON HAKA AULIYA’U DUKA

SU KAYYO SUNKUYO GUN KA

SUNA NEMAN FUYUDAN KA

FA NIMA NA FAKE GUN KA

IN SAM MADADI DA FAIDANI

 

Inji Shehu Abubakar Ateeq Sanka RTA a cikin Tusamma.

 

Magabata sun rayu da yan qadiriyya lafiya lau, tare suke sallah, tare suke maulidi da sauran mu’amala ba tareda kowannen su ya raina kowanne ba.

 

Toh ina kira garemu matasa, musamman mawaqa da masu hawa mumbari domin karanta maulidi, idan kun tashi fadin daraja da martabobin Shehu Tijjani RTA, ku fada cikin ladabi, kar ku qasqantar da kowani waliyyi ballantana sidi Abdulqadir RTA, kamar yadda saboda fadin darajar Annabi ba zaku qasqantar da sauran Annabawa ba.

 

Duk wani waliyyi mai dariqa, sharifi ne, ka ko san zagin sharifi zagin Annabi ne.

 

Dan Allah mu kula, da yawa in kaga dan wata dariqar ya zagi Shehu Tijjani, toh wayanda suke kewaye dashi ne basu da hikimar isar masa da saqon martabar Shehu Tijjani, ko kuma shi din bai da haske RABBANIY.

 

INA SO INJI ZANCEN KA NA’AM YA SHEHU TIJJANI

 

✍ Sidi Sadauki

Share

Back to top button