Allah Baya Karban Aikin Dan Adam Ba Tare Da Soyayyan Manzon Allah SAW Ba.

SHEIKH SANI KHALIPHA ABDULKADIR ZARIA, Yana Cewa:

 

“Idan Ka Gama Had’a Guzurinka Na Zuwa ‘Kiyama, To Ka Tabbatar Ka ‘Daure Shi Da Igiyar ‘SOYAYYAR ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)’,

 

Domin Ita Kad’ai Ce Igiyar Da Masu Bincike Ba Za Su Bincika Ba(Har Su Tsinka Ta), Domin Ya Zamo Kayan Gidan ANNABI(S.A.W),

 

Amma Idan Ka ‘Daure Guzurinka Da Igiyar Wani Ibada(Kamar Sallah Da Sauransu),

 

To Lallai Masu Bincike Ba Za Su Barka Ka Wuce Ba Sai Sun Yi Maka Bincike.

 

Ba Ka Ga Ko Anan Duniya Idan Malamai Za Su Yi Addu’ar Neman Biyan Bukata Su Kan Fara Ne Da Salatin ANNABI,

 

Su ‘Karkare Da Salatin, Su Kuma Bukatun Sai a Sanya Su a Tsakanin Salatan Guda Biyu,

 

Ai Sirrin Shi Ne Fad’in ANNABI(S.A.W) Da Yake Cewa; Addu’ah Tsakanin Salatai Guda Biyu(02) Kar6a66iya Ce Ba’a Mayarwa(Bawa Ita)”.

 

ALLAH Ya ‘Kara Mana Soyayya, Ya Biya Mana Dukkan Bukatunmu Don Albarkar MA’AIKI(S.A.W) Ameeeeen

Share

Back to top button