ALLAH (S.W.T) Ya Kan Yi Kyautar Abubuwa Ga Bayinsa Iri-Iri Ya Kan Bada Mulki Ga Wanda Yake So Da Wanda Baya So. Inji Sheikh Dahiru Bauchi.

LISANUL-FAIDHA(Maulanmu Shehu Dahiru Usman Bauchi(R.A) Yana Cewa;

 

“ALLAH (S.W.T) Ya Kan Yi Kyautar Abubuwa Ga Bayinsa Iri-Iri Ya Kan Bada Mulki Ga Wanda Yake So Da Wanda Baya So, Haka Dukiya, Haka Farin Jini, Haka ‘Daukaka(Kai Komai Ma).

 

Amma Abu ‘Daya Ne Tak Wanda ALLAH Baya Baiwa Kowa Sai Wanda Yake So Kad’ai, Wannan Abu Kuwa Shi Ne; ‘SHIRIYA’ -Shiriya Ita Ce Kadai Wanda ALLAH Sai Wanda Yake So(Yake Bashi),

 

Ma’aunin Shiriya Kuma Shi Ne; ‘IMANI’ Imani Kuma Ba’a Gane Sa Sai Da ‘SOYAYYAR MANZON ALLAH(S.A.W), Iya Gwargwadon Soyayyarka Da ANNABI MUHAMMMADU(S.A.W) Shi Ne Iyakacin ‘Karfin Imaninka Kamar Yanda Ya Zo a Hadisi;

 

Inda Wata Rana SAYYIDUNA UMAR(R.A) Ya Ce; Ya RASULULLAHI! Ina Sonka Fiye Da Dukkan Komai In Banda Raina Dake Tsakanin Hakarkarina, Sai MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Ce; A’a! Da Sauranka Ya UMAR, Sai SAYYIDUNA UMAR(R.A) Ya Ce; To Ina Sonka Fiye Da Ita Kanta Raina ‘Din, Sai MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Ce; To Yanzu Ne Imaninka Ya Cika Ya UMAR, Don Haka; Idan Baka Ji Kafi Son MANZON ALLAH(S.A.W) Fiye Da Rayuwarka Ba, To Imaninka Bai Cika Ba,

 

In Kuma SOYAYYAR ANNABIN Ne Babu Shi, To Hakika Babu Imani Kenan; Komai Sallarka Da Ibadunka, In Babu SOYAYYAR ANNABI MUHAMMADU(S.A.W), To Akwai Garari, Don An Samu Wanda ANNABI(S.A.W) Ne Limaminsa a Bayan ANNABI(S.A.W) Yake Sallah, Amma Ya Zama ‘Dan Wuta Saboda Baya Son MANZON ALLAH(S.A.W),

 

Mu ‘Kara Godewa ALLAH Da Yasa Muka Zama MASOYA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)”.

 

Alhamdulillah!!!

 

ALLAH Ya ‘Kara Mana Soyayyar ANNABI MUHAMMADU(S.A.W)!!!

 

ALLAH Ya ‘Karawa MAULANMU SHEIKH (R.A) Lafiya Da Nisan Kwana Don Alfarmar MASOYINSA (S.A.W). Amiiiin

Share

Back to top button