Allah Ya Karbi Rayuwar Daya Daga Cikin Mahajjatan Jihar Kaduna Hajiya Maryam Ahmad.

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UNN

 

Mahajjaciyar Jihar Kaduna Ta Rasu A Kasar Saudiyya

 

Allah Ya Yi Wa Ɗaya Daga Cikin Mahajjaciyar Jihar Kaduna Wadda Ta Fito Daga Gundumar Igabi Ta Jihar Kaduna, Hajia Maryam Ahmed Rasuwa Ranar Juma’a A Garin Makkah Dake Kasar Saudiya.

 

Majiyar RARIYA Ta Nakalto Cewa An Yi Jana’izarta A Masallacin Harami Dake Birnin Makkah Na Ƙasar Saudiyya Yau Juma’a.

 

Allah Ya Jiƙanta Da Rahma Ya Gafarta Mata, Amiin Yaa ALLAH.

 

Daga Jamilu Dabawa.

Share

Back to top button