Allah Ya Yiwa Jikar Sheikh Dahiru Bauchi RA Rasuwa Sayyada Aishatu Yar Sayyadi Alhaji Ibrahim

Hatsarin Mota Ya Rutsa Da Jikar Sheikh Dahiru Bauchi RA A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja.

 

…..Allah ya yiwa jikan Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sayyada Aishatu yar Sayyadi Ibrahim.

 

Allah ya karbi rayuwar daya daga cikin jikokin Maulanmu Sheikh Dahiru Bauchi RA ya ga Sayyadi Alhaji Ibrahim (Khadimul Faidah) sayyada Aishatu rasuwa sakamakon hatsarin mota daya rutsa dasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja yau asabar 18/02/2023.

 

Muna mika sakon ta’aziyya ga Sheikh Dahiru Bauchi RA, da Khadimul Faidah Sayyadi Alhaji Ibrahim da sauran yan’uwa Musulmai masoya,

 

Allah ya jikan ta da rahma ya gafarta mata, Allah ya karbi shahadar ta. Amiin Yaa ALLAH

 

Daga: Babangida A Maina

  1. Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button