Allah ya yiwa sarkin malaman Zuru Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe rasuwa.

INNA’LILLAH WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN

 

…Allah ya yiwa sarkin malaman Zuru Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe rasuwa.

 

Allah ya yiwa babban malamin musulunci kuma shehun Darikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe Zuru dake Jihar Kebbi a arewacin Najeriya rasuwa,

 

Shehin malamin ya bada gagarumar gudunmuwa a addinin Islama a Najeriya ya kasance mutum mai tawali’u da tsaron Allah tausayi da kuma taimakon addinin Allah,

 

Allah ya jikansa da rahama ya kyautata tamu bayan tasu alfarmar Al’qur’ani. Amiin

 

Daga Abbakar Aleeyu Anache

Share

Back to top button