ALMAJIRAI” sun kasance masu matukar da gudummowa ga wannan kasa ta fuskar: Tattalin arziki, Tsaro, Cigaba, da kuma zaman lafiya.

MUNA GOYON BAYAN KUDURIN SAMAR DA HUKUMAR ALMAJIRAI DA YARA MARASA ZUWA MAKARANTA A MAJALISAR TARAYYA.

 

“ALMAJIRAI” su ma yan kasane dake da hakki kamar kowa, kamar yadda Gobnatin Tarayya da sauran Gobnatoci ke kirkirar hukumomi na kulawa da wasu ba’ari na al’umma haka zalika su na “ALMAJIRAI” sun chanchanci mutumtawa fiye da haka, ta hanyar gina Makarantu, Wuraren kwana da sauransu.

 

ga “ALMAJIRAI” Muna matukar goyon baya Gobnatin Tarayya da na Jahohi su fitar da wani tsari da a ciki za’a hukumantar da sha’anin karatun Allo, ya zamto wanda duk ya kammala haddar Kur’ani, to za’a bashi shaida a hukumance, sannan kuma da bashi gurbin aiki, ko kuma Allowance a kowacce wata.

 

“ALMAJIRAI” sun kasance masu matukar da gudummowa ga wannan kasa ta fuskar: Tattalin arziki, Tsaro, Ci gaba, da kuma zaman lafiya…

 

MUNA KIRA DA BABBAR MURYA GA ‘YAN MAJALISA AKAN SU GAGGAUTA AMINCEWA DA WANNAN TSARI, DAN CI GABAN KASA.

 

ALLAH KA TABBATAR DA WANNAN KUDURI DAN ALFARMAR MANZON ALLAH (S.A.W). ALHAMDULILLAH.

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button