Almajiranci A Najeriya: Laifin Gwamnati Ko Iyayen Yara Waye Mai Laifi ???

LAIFIN IYAYE KO GWAMNATI ???

 

Laifin Duk Na Bangarorin Duka Biyu Ne.

 

Na Farko …..

 

Gwamnati ke da alhakin sanin yanayin karfin iyaye, kafin suyita haihuwa iri iri…

 

Dolene gwamnati tasan Yaya muranen Karkara ke rayuwa, don su fa suna haihuwar Machineries ne na Noma ba wai yaya ba…to amma gwamnati bata aikata hakan.

 

Mafi yawan Yayan da suke bara a gari daga kauyuka suke zuwa.

 

Dolene don magance haka gwamnati ta san meke gudana a karkara don fitar da tsarin taimaka musu da kuma kayyade iyalai ko samar da hanyar daukar nauyinsu. Amma kash Gwamnatu ba tasu take ba…

 

Na Biyu ….

 

Mafi yawan Iyayensu na cikin duhun Jahilalci, su a wurinsu tarun Yaya abun alfahrine, don yawan Yayanka yawan girman gonarka…

 

To zasuyita aure don su tara masu musu ayyuka da kuma fita kunya…

 

A karshe kuma Malamansu ma nada gudumowa akan hakan, don su kan fita kauyuka da kansu don neman a basu Yara wadda a karkashin haka suna bautar dasu…wajen

 

* Noma

* Rubutun sha na kudi

* zuwa wajen Sauka da sauransu…

 

Amma lallai Tsarin karatun Almajirancin na bukatar gudumowar Gwamnati da kuma iyaye baki daya. Allah ya kawo mana sauki. Amiiiin

 

Daga: Kabiru Special

Share

Back to top button