An Aiko Annabi da Manzanci Ne Lokacin Da Ya Cika Shekara Arba’in (40) a Rayuwarsa.
AIKO ANNABI DA MANZANCI S.A.W :
An Aiko Annabi da Manzanci Ne Lokacin Da Ya Cika Shekara Arba’in (40) a Rayuwarsa.
Mala’ika Jibril ya fara zuwa masa ne ranar Litinin goma sha bakwai (17) ga watan Ramadhan a lokacin yana kogon Hira. Kuma ya kasance a duk lokacin da wahayi ya zo masa, ya kan shiga mawuyacin hali, fuskarsa takan canza, kuma Goshinsa yayi zufa.
Lokacin da Mala’ikan ya zo masa a karo na farko, yace da shi:”ka yi karatu” !.
Sai Annabi ya ce : Ni ban iya karatu ba !!.
Sai Mala’ikan ya damke shi da karfi har sanda Annabi ya shiga mawuyacin hali sannan ya sake shi, ya sake ce masa : ka yi karatu !!.
Annabi yace : Ni ban iya karatu ba !!!. haka aka yi har sau uku, ana ukun sai Mala’ikan ya ce da shi :”Kayi karatu da sunan Ubangijinka wanda yayi halitta. Ya halitta mutum daga gudan jini. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne mafi karimci.
Wanda ya sanar (da mutum) game da alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba. [suratul Alaq, Aya :(1-5) ].
Sai ANNABI (S.A.W) ya dawo gurin Khadija a firgice yana bari, ya bata labarin abubuwan da suka faru da shi. Khadija (Allah ya kara mata yarda) sai ta kwantar masa da hankali tace :
Albishirinka !! hakika nasan Allah ba zai tozartar da kai ba har abada, domin kuwa kana sadar da zumunci !, kana fadin gaskiya !, kana daukan nauyin marar galihu !, kuma kana taimakon wadanda masifu suka afka musu.
Daga nan sai wahayi ya yanke, Annabi ya zauna tsawon lokaci wahayi baya zuwa masa. Ana nan a haka sai watarana Annabi yana tafiya cikin garin Makka,
Sai mala’ikan da ya zo masa a karo na farko ya bayyana masa a sama da shi, yana mai kwantar masa da hankali da kuma masa albishirin cewa hakika shi dan aiken Allah ne zuwa ga mutane.
Lokacin da Annabi ya ganshi sai ya firgita ya juya ya koma gida wajen Khadija (R.A) yana cewa :
ku lullube ni !
ku lullube ni !!.
Sai Allah ya saukar masa da wahayi cewa;
Ya wanda ya lulluba da mayafi, Ka tashi domin kayi gargadi wa mutane. Kuma ka girmama Ubangijinka, Kuma ka tsarkake tufafinka”. [suratul Muddassir, Aya:(1-4) ].
Wadannan ayoyi sun kunshi umarni ne ga Annabi daya tashi yayi gargadi wa mutanensa ga barin shirka ya kuma kira su i zuwa ga bautar Allah shi kadai. Daga nan ne fa Annabi yayi damara ya zage damtse ba dare ba rana ya fara kirar yara da manya, maza da mata, ‘ya’yaye da bayi, baki da fari kan azo a bauta wa Allah madaukakain sarki.
Sai aka samu cikin kowace kabila wadanda Allah ya nufe su da shiriya da samun rabo duniya da lahira suka amsa kirarsa, suka musulunta. Kafiran Makka sai suka fara cutar dasu suna gana musu bakar azaba,
Amma Annabi S.A.W Allah ya kare shi ne daga cutarwarsu ta hanyar baffansa Abu-dalib, domin ya kasance mutum ne mai daraja da fada-aji a cikinsu, don haka baza su iya cutar da Annabi da komai ba saboda sun san irin son da yake yi masa.
Imam Ibnul Jauzi yace : Annabi ya zauna a Makka tsawon shekaru uku (3) yana Da’awarsa a boye, bayan saukan fadin Allah ta’ala: Sai ka tsage gaskiya game da abin da aka umarceka dashi, ka kuma kau da kai daga masu shirka. [ suratul Hijri,Aya :(94)],
Sai Annabi ya fara Da’awarsa a bayyane. Lokacin da fadin Allah ta’ala ya sauka : kuma kayi gargadi ga danginka mafiya kusanci. [ suratu Ashshu’ara’I, Aya:(214)].
Sai Annabi ya fito ya hau dutsen Safa yayi kira da karfi yace : “Ya ku mutane na !! sai mutane suka ce wa ye yake kira ?!
Sai akace : ai “Muhammadu” ne, sai suka zo suka tattaru, Annabi yace dasu :
Ya ‘ya’yan gidan wane da Ya ‘ya’yan gidan Abdu manaf, ya ‘ya’yan gidan Abdul-mudallib yanzu zaku gaskatani in nace muku wani doki zai fito ta karkashin wannan dutsen ?!
Sai suka ce : kwarai da gaske, domin kuwa baka taba yimana karya ba, Sai yace dasu : to hakika ni mai gargadi ne agare ku kafin zuwan azaba mai tsanani (ga wanda yaki yin Imani).
Sai baffansa Abu-lahab yace : tir da kai yanzu da ma don wannan kawai ka tara mu, Sai ya tashi ya tafi, sai Allah ta’ala ya saukar da suratul Masad cewa :
Hannaye biyu na Abu- lahab sun halaka kuma ya halaka, har zuwa karshen surar. [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi].
Allah ya bamu Albarkacin su Gaba dayansu bijahi S.A.W. Amiin