An Gudanar Da Jana’izan Masu Zuwa Mauludi Mutun Arba’in 40 A Kaduna, A Mummanan Hatsarin Mota.
An Gudanar Da Sallah Jana’izan Masu Taron Mauludi Mutun Arba’in A Lere Jihar Kaduna.
Daga: BBC Hausa
Wani wanda ɗaya ne daga masu shirya Maulidin ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Lere kan hanyar su ta zuwa Saminaka, inda wata babbar mota ta hau kan motarsu wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da jikkata wasu.
Bayanai daga jihar Kaduna sun ce an yi jana’izar masu bikin Maulidi aƙalla 40 da suka rasu da yammacin ranar Lahadi, sakamakon wani haɗari inda wata babbar motar kaya ta hau kan wata mota ƙirar J5 ɗauke da mutum fiye da 70.
Wani wanda ɗaya ne daga masu shirya Mauludin ya shaida wa BBC cewa “daga garin Kwandari za su zo nan Saminaka a daidai Lere kan kwana wata babbar mota ta hau kan motarsu. An ce wani mai babur ne ya gifta wa direban babbar motar inda shi kuma mai babbar motar ya kauce masa abin da ya sa ya hau kan motar masu Mauludin.”
Bayanan sun ce aƙalla mutum 30 ne suke a asibiti inda suke samun kulawa.
Wani wanda shi ne mutumin da ya ɗauki alƙaluma bayan haɗarin ya ce “waɗanda suka mutu su 41 ne mata guda 19 da ƙananan yara 10 da sauran mutane musamman tsofaffi kusan 11 sai kuma masu rauni fiye da 30.”
Sun tashi ne daga garin Kwandare kan hanyarsu ta zuwa nan, Saminaka. Da isarsu garin Lere, kawai sai wata tirela ta hau kan motarsu,” in ji shaidan.
Bayanai sun kuma ce motar bas ɗin ta ɗauki mutane fiye da kima.
Wani bincike ya tabbatar mana da cewa sama da mutum 1,470 ne suka mutu a zangon farko na wannan shekara, sakamakon hatsari a kan titunan Najeriya,a cewar alkaluman hukumomi.
Hakan ya nuna cewa mutum 16 ne ke mutuwa a kowace rana sanadiyyar haɗarin mota.
Gwamnati ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi na wannan shekara.
Allah ya jikan su da rahma ya gafarta masu, Allah ya kiyaye faruwan haka a gaba. Amiin