An Gudanar Da Sallar Jana’izan Wasu Bayin ALLAH Da Yan Bindiga Suka Kashe A Taraba.

Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

 

Anyi jana’izar wasu daga cikin bayin Allah da iftila’in yan Bindiga ya rutsa dasu a garin Kare kuka dake Gunduma ward a karamar hukumar Gassol A Jihar Taraba.

 

Anyi Sallar jana’izar kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a kofar hakimin Gunduma cikin garin Gunduma da fatan Allah ya jikan su ya gafarta musu.

 

Allah ya karbi shahadarsu ya kawo mana karshen wannan masifar da muke ciki wannan kasa namu Najeriya. Amiin

 

Daga: Muhammad Abdullahi Tutare.

Share

Back to top button