An Kas@he Mana Matafiya Masu Zuwa Ziyara Khaulaq A Kasar Burkina Faso.
WASU DAGA CIKIN FUSKOKIN TIJJANAWA DA SOJOJIN KASAR BURKINA FASO SUKA TASHE.
……Hakikanin Abunda Ya Faru Da Yan’uwa Mu Tijjanawa Matafiyan Zuwa Ziyara Khaulaq.
A ranar laraba ne 1/01/2023, aka samu sanarwan mutawan yan uwan mu Tijjanawa matafiya zuwa ziyaran Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq dake kasar Senegal.
A cikin tawagar wasu daga cikin matafiya sun hadu da shahada inda sojojin kasar Burkina Faso suka fito dasu daga mota suna zargin yan ta’adda ne suka Bude masu wuta har lahira.
Yanda abun ya kasance shine; akwai ganganci tun farko na bin hanyar Kancare, domin hanya ce wanda tun kusan shekaru biyar aka dai na binta saboda matsalar rashin kyan hanyar da kuma yanda ƴan ta’adda su ka mai da ita wajen kafa sansanin su.
Kamar yanda mu ka samu bayani daga ɗaya, daga cikin matafiyan ya shaida mana cewa tun a kan iyaka ta tsakanin ƙasar Burkina faso, da Nijar, sojojin kan iyaka su ka shaida musu cewa akwai ma’aikata yan uwansu sojoji da su ke tahowa daga wani waje kuma sojoji ne masu haɗarin gaske.
Amman lamarin Ubangiji bai saka sun tsaya ba, suka ɗora da tafiya. Ya shaida mana cewa suna cikin tafiya suka haɗu da wata gagarumar rundunar sojoji wanda ya kimta yawan su sun kai kusan mutum ɗari biyar. Yace suna haduwa da su suka tare ɗaukacin motacin su kuma babu tsayawa a nan take suka hau bincike, suna sauke waɗanda suke da siffar kabilar Fulani, da kuma wanda suka ya tara gashi mai yawa, a kansu suna fito da su suna harbe su, ya cigaba da cewa a iya mota ɗaya sun harbe mutane kusan guda takwas a wata mutum biyu jimilar lissafi shi ne an harbe mutane goma sha tara.
Muna kira na musamman zuwa ga Mista Marc Bassey Egbe, jakadan ƙasar Najeriya, a ƙasar Burkina Faso, da ka gaggauta sanar da hukumar ƙasar abin da ya faru a kan kisan gillar da sojojin ƙasar suka yi wa ƴan asalin ƙasar Najeriya.
Sannan kuma muna kira da babbar murya zuwa ga ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje da lallai su binciki wannan al’amari mai cike da rashin imani da rashin tausayi da waɗannan sojoji suka aikata a kan waɗannan ƴan uwa namu. Idan sun kammala bincike da su nemi a hukunta waɗanda suka aikata abin kuma a biya Iyalan waɗanda suka rasu Diya…
A ƙarshe muna roƙon Allah ya karbi shahadar su albarkar shugaba Sallallahu alaihi Wa sallama. Amiin
Daga: Mujaheed M Muhammad