An Samu Karin Wadanda Suke Rasu A Hatsarin Kwale-kwale a Garin Mundi Jihar Niger.
An Samu Karin Wadanda Suke Rasu A Hatsarin Kwale-kwale a Garin Mundi Jihar Niger.
A jiya talata ne aka wayi gari da samun mummanan labarin maras dadi na kifewan masu zuwa taron Maulidin fiyayyen halitta SAW a jihar Niger.
Babban darekta hukumar agajin gaggawa ta jihar Niger, Abdullahi Baba Arah ya ce akwai sama da fasinjoji 300 a cikin kwale-kwalen lokacin da ya kife da masu zuwa taron Maulidi a madatsar ruwa ta Jebba a garin Gbajibo da ke ƙaramar hukumar da yammacin ranar Talata.
Abdullahi Arah ya ce kwale-kwalen wanda ya taso daga garin Mundi zai tafi Gbajibo domin halartar bikin Maulidin Annabi Muhammadu ﷺ cike yake maƙil da mata da ƙananan yara, a halin yanzu an ceto mutum fiye da 150 da ransu Allah ya basu lafiya.
Mutanen daga sassan fadin duniya sun nuna alhinin su akan faruwan lamarin tare da Allah ya jikan wanda suka rasu ya jikan su da rahma.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto ƙarƙashin jagorancin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da sauran mutane.
Ko a watan Satumban 2023, an samu kwatankwacin irin wannan, inda kwale-kwale ɗauke da fasinja 50 ya kife kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 24.
Allah ya bawa wadanda suka ji rauni lafiya, ya kiyaye faruwan lamarin a gaba. Amiin