An Sanya Maulidi Cikin Kundin Tsarin Tarukan Da Za’a Rinƙa Gabatarwa Duk Shekara A Saudi Arabia .

Hukumomin Kasar Saudi Arabiya Sun Sanya Bikin Maulidi Cikin Jadawalin Taruka A Fadin Kasa.

 

A wannan shekara 1444 AH ne hukumomin kasar Saudi Arabiya suka shirya taro na musamman a watan Rabi’ul Awwal (Mauludi) da sunan Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW wanda suka gayyaci malamai sama da ɗari da hamsin 150 waɗanda aka gayyato daga ƙasashe hamsin a faɗin duniya kuma ya ɗauki ƙwanaki ana gabatarwa kuma sukayi ma taron Maulidin da laƙabi da taken:

 

 

 

“ƊA’A TARE DA DARAJOJI A CIKIN RAYUWAR MANZON ALLAH MAI TSIRA DA AMINCI DA KUMA TASIRINSU GA DUNIYA GABA ƊAYA”

 

“القيم الاخلاقية في السيرة النبوية واثرها في قيم السلام العالم”

 

Cikin wadanda suka gabatar da jawabai akwai Maulana Prof. Ibrahim Maqary, shima yana ɗaya daga cikin malaman da aka gayyata kuma ɗaya daga cikin ginshi ƙai a gurin gabatar da taron wanda ya ƙunshi bijiman malamai masu jawabi a yayin gudanar da taron Mauludin.

 

 

 

Tabbas hukumomin Saudi Arabiya sun taka muhimmiyar rawa tare da namijin ƙoƙari gurin yin watsi da halatta ko rashin halattar yin murnar maulidin fiyayyen halitta saw tare da sanya shi a cikin kundin tsarin tarukan da za’a rinƙa gabatarwa duk shekara a kuma cikin watan da aka haifi fiyayyan halitta Annabi SAW.

 

Muna murna ne kawai saboda an girmama fiyayyan halitta Annabi Muhammadu SAW a gurin daya kamata ace nan ne tushen daya kamata su ƙarfafa sha’aninsa, AlhamdulilLah sannu dai a hankali abu nata samun tagomashi fiya da tunanin mu kuma dama munsan a hankali za azo gurin, In shaa Allah.

 

Allah ya ƙara mana ƙaunar Manzon Allah SAW tare da ahalin gidansa da masu biye musu da ƙyautatawa har ya zuwa ranar sakamako, yasa muna cikin cetonsa. Amiin

 

 

 

Daga Imam Anas

Share

Back to top button