An tabbatar da babu wanda yakai Sheikh Abdullahi Uwais sanin ilmin Fiqhu a wannan zamanin.

MALIKUN ZAMANIN MU SHEIKH ABDULLAHI UWAIS LIMANCI (ALLAH YA ƘARA YARDA A GARE SHI)

 

Alhamdulillahi a yau alƙalamin nawa a gida ya samu masauki, domin zai kawo tarihin ƙasaitaciyar rayuwar wanda ya kasance ɗaya daga cikin kyautar Ubangiji da ya yi wannan ƙasa ta mu ta Najeriya, da nahiyar Afirka da kuma duniya baki ɗaya.

 

Kafin na shiga cikin tarihin barin na kawo wata ƴar gajeriyar kissa wanda a gaba na ta faru wanda na ƙara salamawa lamarin Maulana.

 

Allah ya azurta ta ni da halarta Maulidin Sheikh Alhaji Ibrahim Niasee, Allah ya ƙara yarda a gare shi, a unguwar Gyaranya, wanda a ke gabatar da shi a gidan Maulana Sheikh Hamza Lawan Gyaranya, bisa katari da na yi a wannan Maulidin Maulana Sheikh Abdullahi Uwaisu Limanci, shi ma ya samu halartar Maulidin, kafin ya gabatar da jawabinsa sai kawai mu ka ga an fito da Maulana Sheikh Hamza Lawan Gyaranya, zuwa gurin taron, duk da a lokacin jiki ya yi matuƙar nauyi amman haka Maulana Sheikh Hamza Lawan Gyaranya ya yi umarni a fito da shi bayan ya fito bai jima ba ya yi ishara da ba shi abin magana a nan ta ke aka cika umarni aka ba shi abin magana yana karaba sai ya ce:

 

Na yi farin ciki sosai da halartar Malam Abdullahi zuwa wannan bigire kuma ina godiyar Allah da a duk halin da mu ke ciki. Malam Abdullahi wallahi da ina da lafiyar ƙafa da a kullum sai naje wajen ku domin ɗaukar karatu kuma babu fashi amman ina yi wa Tijjani, (Halifa Tijjani) umarni cewa kada ya sake ya gajiya da zuwa ɗaukar karatu wajen ku domin ku kaɗai kuka rage

 

Wannan batu ya sani a cikin tafakuri na tsawon lokaci, domin duk wanda ya san wanene Sheikh Hamza Lawan Gyaranya, a da’irar wulaya ba zai ɗauki maganar da sauƙi ba.

 

An haifi Maulanmu Sheikh Abdullahi Uwaisu Limanci, a cikin unguwar Limanci, wanda tana a kusa da unguwar Madobo, da wanda dukkan unguwanin suna a cikin tsohon birnin Kano, Maulana ya zo duniya a cikin shekarar 1373 Hijiriyya wanda tai daidai da 1954, miladiyya.

 

Mahaifinsa sunansa Uwaisu Ibn Muhammadu Abba Ibn Muhammadu Ɗan Goriba, shi ne mai sarautar Ɗangoriba na farko bayan kafa daular Fulani a Kano, sauratar ta bar gidan su a sakamakon wasiyyar Malam Muhammadu Ɗan Goriba ga ɗansa Malam Muhammadu Abba Kakan Maulana cewa: “Kar ka sake ka karbi wata saurauta ka himmatu wajen neman Ilimin” Bayan rasuwarsa kuma haka ce ta kasance, dalilin rabuwarsu kenan da sarauta.

 

Sheikh Uwaisu Baba, ya kasance shahararren waliyi ne kuma malami wanda yana cikin manyan manyan jagororin malaman garin Kano kuma yana cikin waɗanda suka fara salamawa Shehu Ibrahim Niasse, Allah ya ƙara yarda a gare shi, a cikin gamayyar malaman Kano.

 

Baya ga haka kuma Sheikh Uwaisu, yana ɗaya daga cikin waɗanda su ka fi kowa shan wahala mai yawa a sakamakon wannan sallamawar da ya yi wa Shehu domin ya sha azaba kala-kala daga wajen ƴan uwansa malamai. insha Allahu watarana zan kawo tarihinsa a wannan kafa ta Fesbuk.

 

Mahaifiyarsa sunan ta Sayyada Rabi’atu yar Malam Abubakar Ibn Ishaq Ibn Muhammadu Bashir Ibn Muhammadu Kwaranga, shi kuma ɗan ne a wajen shahararren Malami nan da a ka yi a birnin Kano mai suna Dabo Dambazau.

Kuma shi ne na farkon a sarautar sarkin Bai, a kafuwar daular Fulani, saboda gudunmawarsa na kafuwar daular wanda har yanzu jikokinsa ne su ke dauke da nauyin wannan sarautar.

 

Gidan su Maulana tun asalin gidan Ilimi ne domin da shi ne aka taso tun iyaye da Kakani saboda haka babu bukatar sai faɗi irin kulluwarwa da Maulana ya samu a wajen mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa.

 

Maulana ya fara ɗaukar karatun Alkur’ani mai girma a wajen mahaifinsa wanda yana yawan faɗar cewa “Saboda ba da muhimmanci ga karatun littattafai da a ke so na fara. Karatun Alkur’ani mai girma da sauri da sauri na yi shi domin kullum sai na rubuta Nusuf Hizib kuma na wanke gobe haka zan rubuta na wanke wanda a sati ina samun Hizib biyu da rabi”

Wannan maganar ya ƙara maimaita ta a wata hira da aka yi da shi da gidan jaridar BBC HAUSA..

 

Saboda kada rubutun ya yiwa bari na tsaya sai a rubutu na gaba zan kawo karshen abin da na samu na daga ƙasaitaciyar rayuwar Maulana Sheikh Abdullahi Uwaisu Limanci Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon kwana saboda girman shugaba Sallallahu alaihi Wa sallama.

 

Daga: Mujaheed M Muh’d

Share

Back to top button