An Tono Gawar Dan Tijjaniyya Bayan Shekara 7 Da Mutuwa, Amman Kamar Yau Aka Bunne Shi.

An tono gawar limamin Masallacin Juma’a na Rigasa tare da Dansa dake jihar Kaduna.

 

Lamarin ya faru ne tare da ɗansa Muhammad Zangina waɗanda suka rasu kimanin shekaru 7. Duk a jihar Kaduna.

 

An tono su ne sakamakon hanyar mota express da ta biyo ta kan su wacce gwamnatin jihar Kaduna ke ginawa a unguwar Rigasa kuma bayan tono su da nufin sake musu Kabari sai aka ga tankar yanzu-yanzu.

 

Sannan kuma aka fito dasu daga Makara za’a saka su Kabari don kuwa har ƙamshin Turaren da ake sawa gawa bai gushe daga jikinsu ba

 

Muna fatan Allah ya sa mu cika da imani Ameen.

Share

Back to top button