Annabi Muhammad (SAW) Shi Ya Fara Yin Maulidi – In Ji Sheikh Ahmadu Zariya

Annabi Muhammad (SAW) Shi Ya Fara Yin Maulidi – In Ji Sheikh Ahmadu Zariya.

 

“Shahararren Malamin Addinin Mùsùlùncì mai suna Sheikh Ahmadu (Madahun Nabiyi Zariya) ya bayyana cewa; ƙagaggen sabon abu game da raya watan da aka haifi Manzon Tsira a cikin Mùsùlùncì bai taɓa zama haramtacce ba face halastaccen abune.

 

Jawabin Shehin malamin bai tsaya a nan ba, Annabi shine ya fara yin Maulidi domin ya zo a hadisai kuma Allah (SAW) bai hana Maulidi ba, duba da bai zo a Al-qur’ani Maigirma cewa; abune haramtacce.

 

Bugu da kari Allah (SWA) ya kawo ƙissan Maulidin Annabi Isah (AS) dakansa Acikin Al-qur’ani bare kuma dan mùsùlmì suna kwaikwayo da hakan sai ya zama haramtaccen abu ? don sun yi Maulidin Annabi Muhammadu (SAW).

 

Shehin ya faɗi hakane a yayin da wakilin mu ke zantawa da shi a ranar Zagayen Maulidi a garin Zariya Jihar Kaduna, inda a ƙarshe ya ce; Annabi ya taɓa tara sahabbansa a dai-dai irin wannan wata mai albarka ya raba masu dabino cikin farin ciki da walwala aka yi ta zumunci da juna, ruwayoyi sun bayyana haka da daman gaske, duk a cewarsa.”

Share

Back to top button