ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) Shine Yafi Cancanta Ayi Bikin Tunawa Da Shi Fiye Da Kowa”…Inji Sheikh Dahiru Bauchi RA

NIGERIA @63nd ANNIVERSARY

 

MAULANMU SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI (R.A) Yana Cewa;

 

“NIGERIA Ta Ware Wannan Rana Ta(01 Ga Watan Oktoba) Don Tunawa Da Ranar Da Aka Samu ‘Yancin Kai Yau Fiye Da Shekaru Sittin,

 

Duk Lokacin Da Wannan Rana Ta Zagayo Sai An Shirya Bukukuwa a Ambaci Wasu Mutane Ayi Ta Yaba Musu a Bada Tarihinsu Ace Su Mutanen Kirki Ne,

 

Har Abada Ƙasa Bazata Manta Da Su Ba, Har Ma Wasunsu Ana Liƙa Hotunansu a Jikin Kuɗin Ƙasa Wai Don Dai Sun Sama Ma Ƙasa ‘Yanci,

 

To Jama’a Akwai Fa Wanda Ya Same Mu a Bakin Gaɓar Jahannama Za Mu Afka Ciki Ya Tseratar Da Mu, Bai Barmu Ba Har Sai Da Ya Kaimu Aljanna, Kuma Shi Ne Wanda Ya Karɓa Ma Kowa ‘Yanci Duniya Da Lahira,

 

Shi Ne Mai Cetonmu a Filin Ƙiyama Ba Don Shi Ba, Da Ba’a Yi Hisabi Ba, Shi ALLAH Yake Duba Ya Ji Tausayinmu Wato; ANNABI MUHAMMADU(S.A.W),

 

Don ALLAH Jama’a Akwai Wanda Ya Kamata a Kullum Ayi Murna Da Samuwarsa Irin ANNABI MUHAMMADU (S.A.W),

 

Ayi Ta Bada Tarihinsa Irinsa, Ayita Bukukuwa Irinsa,

 

Ai Ba Wanda Ya Kawo Mana Alheri Irin ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) Saboda Haka Shi Yafi Cancanta Ayi Ta Tunawa Da Shi Fiye Da Kowa”.

 

ALLAH Ya Ƙara Mana Ƙaunar SAYYIDUNA RASULULLAHI(S.A.W), Ya Bamu Albarkar Masu Albarka, Ya Zaunar Da Ƙasarmu NIGERIA Lafiya, Ya Yalwata Arzikinta, Don Alfarmar SHUGABA (S.A.W), Ameeen

Share

Back to top button