Annabi Muhammadu SAW Yace; Wanda Ya Zauna Da Malamin Kamar Ya Zauna Dani Ne.

Wanda Ya Gaisa Da Malami Kamar Ya Gaisa Dani Ne – Inji MANZON ALLAH SAW.

 

Annabi Muhammadu SAW yace; Wanda ya zauna da malamin kamar ya zauna dani ne, ya kuma kara da cewa; Wanda yayi duba zuwa ga fuskar malami duba ɗaya, yafi masa raƙuma dubu na sadaƙa – Inji Ma’aikin Allah.

 

Wanda ya girmama malami kamar ya girmama nine- Inji Ma’aikin Allah

 

Banbancin malami da wanda ba malami ba kamar banbancin wata ne, daran goma sha biyu da taurari -Inji Ma’aikin Allah.

 

Saboda wannan tarin gara ɓasar muke ƙara so tare da ƙaunar malamai musamman irinsu maulana waɗanda babu shakkah sun taro dukkan halayen daya kamata ace malamai sun ɗabi’antu dasu dai-dai gwargwado dan haka babu shakka waɗannan hadisan suna nufin malamai har da irinsu Maulana.

 

Haƙiƙa babu shakka muna sonku, muna ƙaunarku, muna kuma tasirantuwa daku matuƙa, muna roƙon Allah ya karɓi addu’oinka a garemu Maulana.

 

Allah ya saka maku da alkhairi, ya ƙara maku lafiya da jinkiri mai amfani. Amiiiin

 

Daga: Imam Anas

Share

Back to top button