Annabi (S.A.W) ne da kansa ya fara yin Maulidi saboda haka ba bidi’a ba ne – Sheikh Halliru Maraya.

Annabi (S.A.W) ne da kansa ya fara yin Maulidi saboda haka ba bidi’a ba ne – Sheikh Halliru Maraya.

 

Annabi (S.A.W) ne ya fara yin nuni ga murnar ranar haihuwarsa da kansa ~ BBC Hausa @2021.

 

Sheikh Halliru Maraya, daya daga cikin fitattun malaman addini a Kaduna da Nigeria ya ce Annabi Muhammad SAW ne ya fara yin nuni ga murnar ranar haihuwarsa da ake kira Maulidi.

 

“An tambayi Annabi Muhammad SAW dangane da azumin Litinin da ya ke yi. Sai annabin ya ce ranar ne aka haife ni”, in ji Sheikh Halliru.

 

Malamin ya kara da cewa kamata ya yi Musulmi su girmama watan na Maulidi kasancewar a watan ne Allah ubangiji ya bai wa duniya kyautar da babu irinta ga duniya wato haihuwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

 

Abubuwan da ya kamata a yi lokacin Maulidi:

 

Malamin ya lissafa wasu abubuwan da ya kamata a yi a lokacin Maulidi amma wadanda ba su saba da shari’a ba.

 

Taro domin nuna mu’ujizar Annabi da halayensa domin yin koyi da shi

 

Yin azumi

 

Sada zumunci

 

Ziyartar marasa lafiya a asibiti

 

Yin sadaKa

 

Ciyar da jama’a

 

Sai dai malamin ya ce bai kamata a yi duk abin da shari’a ba ta amince da shi ba kamar cakuɗuwar maza da mata, ihuce-ihuce, shaye-shaye da dai sauransu.

 

Rabi’ul Awwal, wata ne na kalandar musulunci da ɓangarorin musulmin duniya ke bikin zagayowar ranar da aka haifi manzon Allah, Annabi Muhammad S.A.W.

 

Musulmai da dama sun yi amannar cewa a watan Rabi’ul Awwal, aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW). Amiin

 

Daga: BBC Hausa

Share

Back to top button