ASARORI GUDA TARA (9) DA ZASU SAMEKA IDAN KA RASA SALLAR ASUBAH ACIKIN JAM’I.

ASARORI GUDA TARA (9) DA ZASU SAMEKA IDAN KA RASA SALLAR ASUBAH ACIKIN JAM’I.

 

 

1. Asarar samun kyakkyawar shaida daga Allah cewar kai kubutacce ne daga chutar Munafurci.

 

ANNABI (S.A.W) “Mafiya nauyin salloli akan munafuqai sune sallar asubahi da sallar isha’i”.

 

2. Asarar babban sanadin shiga Aljannah : ANNABI (S.A.W ) yace “Wanda ya sallaci salloli masu sanyin nan guda biyu, zai shiga Aljannah” _(Sanyayan salloli sune sallar asubah da sallar la’asar”.)

 

3. Asarar samun tsira daga shiga wuta. ANNABI (S.A.W) yace “Duk wanda yayi sallah kafin fitowar rana da kuma kafin faduwarta bazai shiga wuta ba”.

 

4. Asarar samun kulawar Ubangiji : ANNABI (S.A.W) yace “Wanda ya sallaci sallar asubah, to yana cikin alkawarin Allah. ”

 

5. Asarar samun ladan Qiyamul Laili baki dayansa : ANNABI (S.A.W) yace “Wanda ya sallaci sallar isha’i acikin jam’i, yana da ladan tsaiwar rabin dare. Wanda kuwa ya sallaci sallolin isha’i da asubahi acikin Jam’i, to yana da lada kamar wanda yayi tsaiwar dare baki dayansa”.

 

6. Asarar haduwa da Mala’iku da kuma samun shaidarsu : ANNABI (S.A.W) yace : “Akwai Mala’ikun dake bibiyar juna acikinku, wasu Mala’ikun da daddare, wasu kuma da rana.

 

Kuma suna haduwa ne alokacin sallar asubahi da la’asar. Sannan wadanda suka kwana acikinku sai su tafi zuwa sama, Sai Allah ya tambayesu alhali ya fisu sani, “Shin yaya kuka baro bayina?”.

 

Sai suce “Mun barosu alhali suna yin sallah kuma yayin da muka zo garesu ma mun samesu ne suna yin sallah”.

 

7. Asarar samun haske da kyalkyali aranar Alkiyamah : Annabi (S.A.W) yace : “Kayi albishir din samun cikakkken haske aranar Alkiyamah ga wadannan dake yin tafiya zuwa Masallatai acikin duhu”.

 

8. Asarar samun lada wanda yawansa da girmansa yafi duniya da taskokin cikinta : ANNABI (S.A.W) yace “Raka’atayil Fajri (raka’o’i biyu da akeyi kafin sallar asubah) tafi alkhairi fiye da duniya da abin cikinta”.

 

Wannan fa ladan sallar nafila lr asubah kenan, to yaya kuma darajar sallar farillar asubah da kanta ?.

 

9. Asarar alkhairai da albarkoki masu yawa, ga kuma asarar lada.

 

ANNABI (S.A.W)yace “Da ace mutane sun san abin dake cikin sallolin isha’i da sallar Asubah da sun rika zuwa garesu koda da jan-ciki ne (ko rarrafe).

 

Wanda ya zauna agida bai halarci sallar asubahi acikin jam’i ba, ya samu ribar barci da minshari mai yawa.

 

Amma Muminai kuma sun ribaci lada mai yawa wanda yafi duniya da kayan cikinta.

 

Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W). Amiiiin Yaa ALLAH.

Share

Back to top button