AYI HATTARA: Sheikh Dahiru Bauchi RA Yana Cikin Koshin Lafiya, Labarin Karya Ake Yadawa.

AYI HATTARA: Sheikh Dahiru Bauchi RA Yana Raye Bai Mutu Ba, Labarin Karya Ake Yadawa.
Al’ummar Musulmai tare da masoya daga sassa daban-daban na fadin Najeriya dama duniya suna kira don tabbatar da sahihancin wani labari da suka gani a shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter cewa Allah ya karbi rayuwar shahararren malamin addinin Islama Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA.
Hakikanin gaskiyar magana wannan labarin ba gaskiya bale, kuma bata da tushe balle makama (Fake News) ne.
An rubuta labarin rasuwan ne a shafukan sada zumunta na mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari da Kuma dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alh Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) suna addu’an fatan samun sauki bashi da lafiya.
Alhamdulillahi Maulana Sheikh yana cikin halin lafiya sai dai jiki irin na girma. Alhamdulillah
Muna Addu’an Àllah ya karawa Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA lafiya da nisan kwana albarkacin Manzon Allah SAW.
Daga: Babangida A. Maina
Tijjaniyya Media News