AZUMIN ASHURA; Wannan Ranar Itace Ranar Goma (10) Da Watan mMuharram Na Ko Wace Shekara

AZUMIN RANAR ASHURA

 

Wannan ranar ita ce ranar goma (10) da watan muharram na ko wace shekara.

 

Watau asalin wannan azumi tun kafin zuwan musulunci ne Kuraishawan Jahiliyya su ke yinsa.

 

An ce da shi ne Azumin da aka wajabta har sai da aka rubuta wa Al’umma Azumin Ramadan sai shi kuma ya zama na nafila.

.

Yahudawa sun kasance suna azumin goma da watan tevet watau watan goma na shekaransu domin godiya.

 

Amma an samu sabani tsakaninsu a dalilin da yasa aka wajabtachi akan su. Da musulunci ya zo sai ya bayyana dalilin cewa wannan ranar farin cikice da kuma godiya ga Allah domin ranar da Allah Ya tsirar da Annabi Musa da mutanensa da ga Firauna.

 

Saboda haka ANNABI S.A.W yace:- mu musulmi mun fi chanchanta da Annabi Musa saboda haka yayi umurni da muyi azumin.

 

To ya yan uwa maza da mata, a lokacin da muke yin wannan azumi wanda ya dace da ranar Asabar ko kuma Lahadi mu roki Allah Madaukaki da ya kubutar da mu daga wadannan kananan firaunoni wadanda suke watsa barna acikin kasar mu, Kuma yakamata mu yalwata wa iyalenmu da abinci mai yawa da inganci kamar yadda yazo a wanni Hadisi ko da yake mai rauni ne.

 

Wannan ranar farin ciki ne da kuma ibada da jin dadi. Babu wurin bakin ciki ko bacin rai a wannan ranar.

.

Kuma mu sani fa Allah Mafi karfi yana sane da abunda ashararun mutane da azzalumai suke yi. Yana musu jinkirine domin su kara zurmawa cikin zunubi.

 

Ana so mutum ya kara da ranar 9 ko kuma 11 ya hada da ta ashura, ko ko kuma ya yi azumin kwana ukun wandan yafi hakanan.

 

Amma ga wanda akwai azumin ramkuwa wato na Ramako na Ramadan akansa, Imam Malik yafi rinjayar da gabatar ramuwar akan ashura domin Allah yafi son a cika farilla da yin nafila.

 

Allah ya shiryar damu gaba daya. Amin

Share

Back to top button