Ba Jami’a Bace, Kuma Ba Makarantar Boko Bace, Kai Ba Makarantar Kudi Ba Ce, Tsangayar Almajirai Ce A Gombe.

Ba Jami’a Bace, Kuma Ba Makarantar Boko Bace, Kai Ba Makarantar Kudi Ba Ce, Tsangayar Almajirai Ce A Gombe

 

Daga Haji Shehu

 

A kokarinta na ganin ta samarda ilimi bai daya wa Al’umma, gwamnatin jihar Gombe ta himmatu wajen sauyawa Manyan Tsangayun Almajirai Fasali domin yin gogayya da zamani.

 

Wannan yunkuri na gwamnatin Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, yana gudana ne karkashin Hukumar Besda wanda Dr. Ahmed Bappah Abdullahi ke jagoranta, ganin kowanne Yaro ya samu ilimi musamman yaran dake tangaririya a gari.

 

Baya ga canza Fasalin Tsangayun zuwa dai-dai da zamani, hukumar Besda ta samarda Malamai wadanda suke koyarda Almajirai karatun Boko bayan kammala karatun Addini a kowacce rana.

 

Kamar yadda mai karatu yake gani wadannan hotuna sune na Tsangayar Farko da aka kammala aikin ta, wato Tsangayar Gwani Sani dake fadar jihar Gombe, inda aka gina:-

 

Ɗakin Kwanan Almajirai – 16

Gidajen Malamai – 3

 

Manyan Dakunan Karatu – 8

Katafaren Masallacin Juma’a

 

Babban Wajen Cin Abinci

Bandaki – 36

 

Gadon Kwana Almajirai – 612

Shirin wanda yake karkashin kulawar hukumar BESDA zai cigaba da fadaduwa zuwa lunguna da sako na jihar Gombe domin inganta karatun Almajiranci yayi daidai da zamani.

 

Haji Shehu

10-Aug-2022

Back to top button