Babban Limamin Oyo, Sheikh Mashood Abdul Ganiyy Adebayo Ajokidero III Ya Rasu.

Babban Limamin Oyo, Sheikh Mashood Abdul Ganiyy Adebayo Ajokidero III ya rasu.

 

Daga: Babangida A. Maina

 

Shahararren malamin Musulunci kuma shehin darikar Tijjaniyya a kudancin najeriya Sheikh Mashood Abdul Ganiy Adebayo Ajokidero III ya rasu a birnin Ibadan jihar Oyo.

 

Jaridar Tijjaniyya Media News ta ruwaito cewa ya rasu ne da sanyin safiyar yau alhamis 26/01/2023, Sheikh Mashood Abdul Ganiy Adebayo Ajokidero shahararren malamin tsangaya addinin islama ne a fadin najeriya wanda ya bada gagarumar gudumawa wurin daukaka Addinin Musulunci a kudancin najeriya.

 

Muna addu’an Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa, Allah ya karbi shahadar sa. Amiin

 

Daga; Babangida A. Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button