Babban Malamin Islama A Duniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA Yana Cewa;

LISANUL-FAIDHA (Maulanmu Sheikh Tahiru Usman Bauchi(R.A) Yana Cewa:

 

“Abin Da Mutum Bai Sani Ba Guda Biyu(02) Ne Na Farko; Abin Da Baka Sani Ba Bai Dame Ka Ba, Wannan Babu Ruwanka Da Shi, ALLAH(S.W.T) Yana Maka Gargadi Da Cewa:

 

“Walataqfu Ma Laisa Laka Bihi Ilmun”,

 

Sai Na Biyu Shi Ne: Abinda Baka Sani Ba, Kuma Ya Dame/Shafe Ka, Kana So Ka San Shi Wannan Shima ALLAH(S.W.T) Yana Baka Shawara Cewa;

 

“Fas’alu Ahla Zikri In Kuntum La Ta’alamun…”

 

SHEHU(R.A) Ya ‘Kara Da Cewa;

 

…Duk Lokacin Da Mutum Ya Ce Zai Yi Magana Cikin Abin Da Bai Sani Ba, To Zai Zamo Jahili Mahaukaci”.

 

ALLAH Ya Kiyaye Mu Son Zuciya, ALLAH Shi Kiyaye Mana Imanimmu

 

ALLAH Ya ‘Karawa MAULANMU SHEHU(R.A) Lafiya Don Alfarmar MA’AIKI (S.A.W) Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button