Babban Malamin Islama Kuma Jigo A Darikar Tijjaniyya Masani A Fannonin Ilimin Addini.

Wannan Shine Sheikh Ibrahim Aliyu Gajali Gombe, Malami masanin addini kuma muatafanini masani na fiqh, hadisi, lugga, sarfu uwa uba tasawwuf, masanin alƙur’ani da tafsirinsa.

 

Ya kasance shehin ɗarikar Tijjaniyya mai tarbiyyantar da al’umma daga ciki da wajen jihar Gombe kan soyayyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam da kuma bin sunnarshi, ya kasance mai horo da bin Allah a duk cikin karatuttukanshi.

 

Shine shahararren malamin da ya karance littafin Ashafa a gidan rediyon Progress dake nan jihar Gombe. ya ƙarar da rayuwarsa cikin hidima ga Addinin Musulunci da al’umma ba dare ba rana.

 

Ya bada gudummawa sosai wajen haɗin kan ƴan uwa musulmai ba ƴan ɗariƙa kaɗai ba. Ya kasance wakilin al’umma na ƙwarai da yake isar da haƙiƙanin saƙon da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam yazo da shi.

 

Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana Albarkacin Shugaban Halitta Sallallahu Alaihi Wasallam. Amin

 

Mustapha Abubakar Kwaro

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button