Babban Malamin Musulunci Sheikh Ibrahim Inyass RA Ya Cika Shekaru 47 Da Rasuwa.

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYASS RA.

 

….Babban Malamin Musulunci Sheikh Ibrahim Inyass RA Ya Cika Shekaru 47 Da Rasuwa.

 

Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq an haife shi a ranar (26/07/1900) a kasar Senegal, mahaifin sa Alhaji Abdullahi Tijjani, Sheikh Ibrahim ya kasance shugaba kuma jagoran sufanci da darikar Tijjaniyya a Senegal da yammacin Africa.

 

Ya tashi bisa kularwar mahaifinsa, ya haddace Alkur’ani mai girma a hannun mahaifinsa A cikin kananan shekaru Yafa wallafa littafi yana da shekaru 21 a duniya.

 

Sheikh Ibrahim Inyass yana da mabiya masu dumbin yawa a duniya, mabiya darikar Tijjaniya ya kasance mutun mai muhimmancin a cikin rayuwar mabiyan sa wurin koyi da halayensa da dabi’unsa a cikin rayuwar su. Anyi masa shaida da soyayyan Annabi ﷺ. Da kuma riko da sunnar Manzon Allah SAW.

 

Sheikh Ibrahim Inyass shi ne dan Afirka ta Yamma na farko da ya jagoranci sallar a babban Masallacin Al-Azhar a Masar , bayan da aka yi masa lakabi da “Sheikh al-Islam”. Kuma malami na farko da Sarki Faisal na Saudiyya ya ziyarta a kauyen sa (Kaolack) a Senegal.

 

Sheikh Ibrahim Inyass mutumin Afirka ne, ya kasance dan gwagwarmayar neman ƴanci a Afirka ta Yamma, saboda gudummawar da ya bayar don samun’ Ƴanci a Ƙasashen Afirka. Ya kasance aboki kuma mai ba da shawara ga Shugaban Ghana na farko, Kwame Nkrumah, da aboko Ga Gamal Abdel Nasser da Sarki Faisal na Saudi Arabia. Kuma Sheikh Ibrahim kasance Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya tare da Faisal a matsayin Shugaba.

 

A shekarar 1937 lokacin da suka haɗu da Shaykh Ibrahim a lokacin aikin Hajj a Makkah, Sarkin Kano, A Najeriya, Alhaji ‘Abdullahi Bayero ya yi mubaya’a ga shehin kuma ya bayyana kansa a matsayin almajirin Sheikh Ibrahim. Wannan lamarin ya sa Sheikh Ibrahim ya sami amincewar da yawa daga fitattun shugabannin Tijānīyyah A Arewacin Najeriya da ma wasu da dama wadanda ba Yan Darikar ba.

 

Alhaji Abdulmalik Atta basarake ne daga Okene kuma Babban Kwamishina na farko a Najeriya A Kasar Ingila, yana daya daga cikin manyan almajiran Sheikh Ibrahim da kuma surukin shehin ta hanyar ‘yarsa Sayyida Bilkisu. Shaykh Ibrahim ya zama sanannen kuma jagoran darikun sufaye) a ko’ina cikin yankunan Kasar Hausa na Yammacin Afirka. Yana da miliyoyin Almajirai a duniya, yayi rubuce-rubuce da dama kusan sama da 75 a rayuwar sa.

 

Sanadiyar Shehu Ibrahim Inyass RTA Ne Gwamnatin Najeriya Ta Sanya Hutun Maulidi Ya Zamo Doka A Kasa, Bayan Shehu Ya Zo Taya Najeriya Murnan Samun ‘Yanci A Shekarar lokacin ya gana da Firar minista na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, sai Shehu ya bashi shawara cewa tunda kai Musulmi ne, ya kamata ka sanya ranar Maulidi ya zamo ranar hutu a Najeriya.

 

Sheikh Ibrahim Inyass mabiyin addinin Islama, Mazhabar Maliki, Akida Ash’ariyya, Darikar Tijjaniyya. Sheikh Ibrahim Inyass ya rasu ranar 26 Yuli 1975 (shekaru 74) a wani asibitin St Thomas’ Hospital, London, dake kasar United Kingdom. Ya rasu yabar maza da mata da yawa da dama da kuma almajirai a sassan duniya da mabiya masa da miliyan 50.

 

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa ya jaddada rahma a gare shi Albarkacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaili Wasallam. Amiin

 

Rubutawa Da Tattarawa;

Babangida Alhaji Maina (Tijjaniyya Media News

25/07/2023 – 7/Muharram/1445.

Back to top button