Babban Shehin Malami Kuma Jigo A Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru 101 A Duniya Lissafin Hijiriyya.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR Ya Cika Shekaru 101 A Duniya Lissafin Hijiriyya.
Sheikh Dahiru Bauchi OFR RA, sanannen malamin Islama ne da yayi suna a nahiyar Afirka baki daya saboda hidimarsa ga addinin Musulunci Shehin malamin na da shekaru 101 Hijjah Miladiya a duniya.
Kuma shehin malamin yana da yara 80, Malamin ya bayyana cewa a cikin yara 80 guda 70 duk sun haddace kur’ani mai tsarki.
Shehin ya rubuta kur’ani sau biyu, da hannun sa yana kan na ukun kuma ya yi aikin hajji fiye da 50 a duniya da aikin Umrah fiye da 100.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi babban shehin darikar Tijjaniya ne da ake ji dashi a duk fadin nahiyar Afirka.
Ya sadaukar da rayuwarshi wajen hidimtawa Al-Qur’ani ta hanyar koyar dashi ga jama’a, Yana da makaratu a duk jihohin Arewacin Nijeriya dama yammacin Africa.
An haifi shehin malamin a ranar 28 ga watan Yuni 1927 ko 1924 wanda ya yi dai-dai da 2 ga watan Muharram 1346. Ko 1344, Bisa sabanin Lissafi.
An haifeshi a garin Nafada da ta ke jihar Gombe a halin yanzu kuma shine dan fari a wajen mahaifin sa, Shekh Dahiru Usman Bauchi Cikakken bafulatani ne gaba da baya. Sunan mahaifiyar sa Maryam ‘yar Ardo Sulaiman, mahaifinshi sunanshi Alhaji Usman dan Alhaji Adam.
Shehin malamin ya haddace kur’ani a wurin mahaifinsa inda daga baya ya tura shi Bauchi don neman tilawa. Malamin ya yi auren fari a 1948 lokacin yana da shekaru 20 a duniya
Sheikh Dahiru ya ce yana da ‘ya’ya kimanin 80 kuma 70 daga ciki sun haddace kur’ani. Wasu daga ciki sun haddace tun suna da shekaru 7 a duniya, tun kafin su iya rubutun allo.
Kuma yayan sa kan fita kasashen duniya don karatun fannonin addini har da na boko. Akwai Daraktoci a cikin ‘ya’yana a yanzu,”
Sheikh Dahiru Bauchi na da mata hudu, duk da wasu sun rasu, wasu kuma dq yawa sun fita.
Sheikh Dahiru yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani.
cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda suka karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.
Sheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.
Shehin malamin Yace abin da ya fi bashi sha’awa a rayuwarsa shi ne irin yadda ya mayar da Alkur’ani sana’arsa da kuma yadda ya rungumi Darikar Tijjaniya ta zama rayuwarsa.
Allah ya kara ma rayuwa albarka, ya karawa Maulana Sheikh lafiya da nisan kwana. Amiin Yaa ALLAH