BABBAN TASHIN HANKALI: Watarana Mala’ika Jibreelu (A.S) yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) a wani lokacin da bai saba zuwa masa ba.

BABBAN TASHIN HANKALI!!!

 

Hadisi ne zan karanta muku Amma ina neman alfarma guda awajenku kafin ku karanta Hadisin nan, Alfarmar da nake nema awajenku ita ce, ku tsayar da duk abinda kukeyi, ku nutsu ku karantashi da kyau.

 

Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani.

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Karshe, da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya.

 

Yazeedur Raqqaashiy ya karbo Hadisin daga Anas bn Malik (R.A) yana cewa: Watarana Mala’ika Jibreelu (A.S) yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba.

 

Yazo, gaba dayan launin fuskarsa ya canza. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa “MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA CANJA HAKA?”. Yace “Ya Muhammadu (S.A.W) nazo maka ne awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu hura wuta suci gaba da Hura ta.

 

Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Kabari gaskiya ce, kuma Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamata yayi wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa ya samu tsira daga wannan”.

 

Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa “YA JUBREELU INA SO KA SIFFANTA MUN YADDA JAHANNAMA TAKE”.

 

Sai yace “Na’am. Hakika Allah madau kakin Sarki yayin da ya halicci Jahannama, yasa an hurata tsawon Shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA -JAWUR.

 

Sannan aka sake hurata tsawon Shekaru DUBU har sai da ta zama FARI – FAT!!

Sannan aka sake hurata tsawon shekaru DUBU har sai da ta zama BAKA – KIRIN!!!.

Tana nan har yanzu BAKA KIRIN ce, mai

tsananin duhu ce.Harshen Balbalinta basu mutuwa ballantana Garwashinta.

 

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za’a bude misalin kofar allura daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan Ma’abotan doron duniyar nan sun kone baki dayansu saboda tsananin zafinta.

 

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za’a ratayo tufafi guda daya tufafin ‘Yan Wutar Jahannama a makaloshi atsakanin Sararin Samaniya, da sai Dukkan Ma’abotan doron kasa sun Mutu baki dayansu saboda tsananin.

 

Ya Allah ka karemu daga dukkanin azabarka kasa muyi kyaky kyawan karshen Ya Hayyu Ya Qayyum

Back to top button