BABBAR MAGANA: Babu Wani Abin Da Muka Rike A Zawiyoyyin Mu Na Tijjaniyya Fiye Da Alqur’ani.

Babu Wani Abin Da Muka Rike A Zawiyoyyin Mu Na Tijjaniyya Fiye Da Alqur’ani

 

Cewar Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria

 

Abinda ake fara koyawa yaro a zawiyoyin Tijjaniyya shine haddar Alqur’ani. Bayan yaro ya samu haddar Alqur’ani sai ya fara karatun Ilimi duk a cikin Zawiyya. Dan haka zawiyyoyin mu na Tijjaniyya tamkar wasu manyan Jami’oin ilimi ne, Alhamdulillahi kusan a yanzu babu wasu jama’an da suke da yawan mahaddata Alqur’ani kamar jama’ar Tijjaniyya.

 

Saboda haka maganar cewa yan tijjaniyya nada wani littafi wanda yafi Alqur’ani kagaggiyar karya ce na fasikai makiya ahlul zikir, domin da muna da wani abin da yafi Qur’ani da shi zamu fara koyawa yara kamin Alqur’ani.

 

Babban jahilcin da yasa suke fadin haka shine, rashin iya rarrabe tsakanin Falala da Daraja. Sun dauka kalmar تعدل da تفضل ma’anarsu daya ne.

 

 

Daga: Ibrahim Sani Khalifa

Share

Back to top button