“Babbar Wasiyyar Da ALLAH Ya Bar Mana; Babu Kamar Jin TSORON ALLAH.

LISANUL FAIDHA(Maulanmu Shehu Dahiru Usman Bauchi(R.A) Yana Cewa:

 

“Babbar Wasiyyar Da ALLAH Ya Bar Mana; Babu Kamar Jin TSORON ALLAH;

 

Domin ALLAH Ko Bai Ce Aji Tsoronsa Ba, To ALLAH Abin Tsoro Ne, Amfanin Hudubar (Da Ake Yi Mana Kullum Juma’ah Kenan) Ake Mana Wa’azozi a Tuna Mana Inda Muka Fito Da Inda Zamu Tafi (a Fad’a Mana),

 

Halin Mutanen Kirki Da Sakamakonsu a Fada Mana Halin Mutanen Banza Da Sakamakonsu, In Ka Aikata Aikin Kirki Ka Tsira,

 

In Kuma Ka Aikata Munanan Ayyuka Ne To Zaka Ga Sakamako Dai Dai Da Abinda Ka Aikata;

 

‘INNAL ABRARA LAFI NA’IM WA INNAL FUJJARA LAFI JAHIM’

 

Saboda Haka Mu Kula Mu Ji Tsoron ALLAH, Mu Yi Ayyuka Na Gari Musammanma Yawan Zikirin ALLAH Shi Ne Babbar Sunnar MANZON ALLAH (S.A.W) Kamar Yadda Qur’ani Mai Girma Ya Fada Mana,

 

Sannan Mu Yawaita Yawan Salatin MANZON ALLAH(S.A.W), Mu Yawaita Istighfari, Mu Yawaita Fadin; La Ilaha Illallahu Su Ne Dukiyar/’Kudin Lahira”.

 

NA’AM SHEHU

 

FATANMU DAI A KULLUM SHI NE ALLAH YA ‘KARAWA SHEHU LAFIYA DA NISAN KWANA, YA BA MU ALBARKARSU AMEEEEN.

 

ALLAH YA ‘KARA MANA TSORON ALLAH A ZAHIRINMU DA BADININMU AMEEEN

Share

Back to top button