Babu gurin da nake jin dadin kasancewa kamar gurin Maulidin Manzo S.A.W ” ~ Sarkin Bichi

Babu gurin da nake jin dadin kasancewa kamar gurin Maulidin Manzo S.A.W ” ~ Sarkin Bichi

 

Mai Marataba Sarkin Bichi, Alh. Nasiru Ado Bayaro, ya ce babu wajen da yake jin dadin kasancewar sa a Duniya face wajen taron Maulidin Annabi S.A.W.

 

Alh. Nasiru Ado Bayero, ya bayyana hakane a daren Asabar a wajen taron Maulidin da Mahmud Sa’eed Adahama, ya shirya a Unguwar G.R.A da ke Kano.

 

Mai Martaban ya ce, ” ba karamin farin ciki yake ji ba, idan akace ya halarci taron maulidi “.

 

Daga cikin wadanda suka halarci Maulidin, akwai Shugaban majalissar Shura ta jihar Kano, Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, inda ya ce rashin shugabanci na gari da bin doka da Oda da kyakkyawar mu’amula, wasu muhimman abubuwa ne da sai an gyara su za’a samu Al’umma ta gari.

 

Taron Maulidin da aka gudanar cikin Sa’o’i dai, ya maida hankali ne kan kara bayyanawa Al’umma daraja da girman da Manzo S.A.W ke da shi a wajen ALLLAH madaukakin Sarki, kamar yadda masu jawabi su kayi.

 

Daga Nazeer Bashir Tsamiya.

Share

Back to top button