Babu Shakka Anyi Kazamar Aika-aika a Kaduna a kan masu Mauludi ba basu yi kama da yan ta’adda ba ka kowanne fusta.

Sakon Sheikh Imam Ibrahim Maqari Hafizahullah Akan Kis@an Ta’a@ddacin Akan Masu Gudanar Da Mauludi.

 

Mun tabbata Sojoji su na ƙoƙari wajén karé rayukan mutanen ƙasa.

 

Suna kutsawa haɗari, su na rasa rayukan su domin neman kiyaye rayukan talakawa.

 

Sai dai akwai matuƙar sakaci wajen samar ma su da dukkan abubuwan da su ké buƙata domin gujé wa tafka kurakurai cikin hare-haren su ga ɓarayin jeji da sauran miyagu.

 

Babu shakka an yi ƙazamar aika-aika a Kaduna a kan mā su Maulidi da ba su yi kama da ƴan ta’adda ba ta kowace fuska, kuma za a iya kaucé wa faruwar irin wannan aika-aika idan an bi matakan da su ka dacé.

 

Ya wajaba hukuma ta ɗauki alhakin biyan diyyar waɗanda su ka rasa rayukan su da maganin waɗanda su ka jikkata.

 

Muna fata wannan kuskure ba zai sanyaya gwiwar sojojin mu ba wajen ganin sun tsaftace dazukan mu daga ɓarayin jéji da sauran ƴan ta’adda.

 

Kamar yadda muké fata, hukuma zata miƙe tsayé wajen tabbatar da ƙananan sojoji su na samun duk irin horo da makamai da su ké buƙata domin taƙaita kura-kurai wajen aiwatar da aikin su.

Share

Back to top button