Babu Wata Hujja Dake Nuna Salati Ibrahimy Yafi Kowane Salati Inji Albani

Babu wata Hujja dake Nuna Salati Ibrahimy yafi kowane Salati Inji Albani!!

 

Kwana biyu naga yadda Triumph ya dasawa mutanen mu wata Fahimta da Molanka da kuma Aɗifa, inda yake nuna duk wani Salati da ba Ibrahimy ba Bidi’a ne balle kuma ace ga wani Salati da yafi Salati Ibrahimy.

 

Na farko kiran ƙirkirar Salati da bidi’a ƙoƙarin bidi’antar da mafi yawan Sahabbai daga ciki harda Sayyadina Aliyu R.T.A domin kuwa yazo cewa ya ƙirƙiri Salatin sa:

 

اللهم داحي المدحوات وبارئ المسموكات اجعل سوابق صلواتك، ونومي بركاتك وزائد تحيتك على محمد عبدك ورسولك.

 

Haka Abdullahi Bin Mas’ud duk sanda zeyi Salati yana yin Salatinsa ne ba Ibrahimy ba Salatin Shine:

 

اللهم اجعل صلواتك وبركاتك ورحمتك على محمد عبدك ورسولك، إمام الخير ورسول الرحمة.

 

Shin wadannan Sahabban suma yan bidi’a ne, ko basusan da Salati Ibrahimy bane !?

 

Sannan Albani nasu ya tabbatar da cewa babu wani Nassi da akayi Naƙalinsa da yake nuni da cewa Salati Ibrahimy yafi kowane Salati bari dai yayi nuni da cewa ta ɓangaren Ma’ana Salatin Shafi’iyyawa ya fishi:

 

اللهم صل على محمد كلما ذكره الذاكرون وسها عن ذكره الغافلون.

 

Wanda Agun Shafi’iyyawa ko rantsuwa kayi zakayi Salati nasu zakayi inda Nawawy yace: aaa Ibrahimy za’a yi, sannan Albani yayi wa Nawawy Raddin cewa da yawa daga Malamai sun mai ta’aƙibi akan haka sun nuna baida hujja.

 

A Taƙaice Albani yace: babu wani Hadisi ko wata magana da aka Naƙalto da take nuni da cewa Salati Ibrahimy yafi kowane Salati, ta gun Ma’ana kuwa na Shafi’iyyawa ma yafi Salati Ibrahimy.

 

Wannan yasa muma muka ce in za’a duba ma’ana Salatil Fatih yafi Ibrahimy Saboda ya tattaro yin Salati ga Annabi S.A.W ne حق قدره ومقداره العظيم Gwargwadon Girmansa da Miƙdarinsa, to wane yasan iya girman Annabi S.A.W.

 

Albani zaku yiwa Raddi ba Mal. Abulfathi Assany ba.

Share

Back to top button