Banbancin Masu Shirya Tarukan Walimar Siyasa Da Tarukan Mauludi

KU SUFAYE KU GODEWA ALLAH.

 

Idan ka dauki dubban kudade ka baiwa biri, da kwayar Ayaba guda, mai yiwuwa sai ya yayyage wadannan kudaden, ya dauki Ayaba guda, alhali wadannan kudaden zasu sayi dubban Ayaba da zai dauki lokaci yana mora.

 

To amma kai da kasan amfanin Kudaden, kaga idanunka basu ma zuwa kan wannan Ayabar guda, balle ka shagala da ita.

 

To haka abin yake ga wadanda suka fahimci girman MANZON ALLAH (S.A.W) suke Shirya tarukan Mauludinsa, da wadanda suka fahimci girman wasu ababen Duniya suke shirya tarukan nuna murna akansu, ta hanyar kyarar yi ga MANZON ALLAH (S.A.W).

 

Yadda bazaka iya ganar da Birrai gane Muhimmancin kudaden nan sama da Ayaba guda ba, haka zalika suma wadannan bazaka iya ganar dasu Muhimmancin nuna soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) da godewa ALLAH a wannan Janabi sama da wanin hakan ba.

 

Face dai yadda wadannan Birran zasu yayyaga wadannan kudaden, suma haka zasuke yayyaga muku mutunci saboda nuna soyayyarku ga madaukakin da babu kamarsa.

 

KU GODE ALLAH DA ALLAH YA ZABE KU YA FAHINTAR DA KU GANE GIRMAN WANDA YAKE GIRMAMAWA, KUMA KU ROKAR MUSU ALLAH SUMA YA GANAR DA SU GANE HAKAN. AMIIIIN YAA ALLAH.

 

Daga: Muhammad Usman Gashua

Share

Back to top button