Bidi’a mafi tsufa da muni a tarihin Musulunci ita ce Bidi’ar kafirta ma’abuta La’IlaHa IllaL-Lah.
Maulana Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari Hafizafullah babban limamin masallacin Abuja, Nigeria. Yana cewa;
Farfesa Ibrahim Maqari Hafizafullah ya rubuta a shafin sa na Facebook Page din sa, inda yake jawo hankalin al’ummar Musulmai baki daya, inda ya bayyana kamar haka;
2. Bidi’a mafi tsufa da muni a tarihin Musulunci ita ce Bidi’ar kafirta ma’abuta La’IlaHa IllaL-Lah
Magabata na ƙwarai basu zargin mujtahidi da saɓo, koda kuwa ijtihadin nan cikin asalolin Addini ne, kuma yayi kuskure.
2, Duk mujtahidi yana da ladar ijtihadinsa. Idan ya dace yana da ƙarin lada na dacewa, idan yayi kuskure babu zunubi akansa.
3, A asibitin gyaran zuciya, mai hassada ɗaya ne daga cikin marasa lafiya.. Aikin likita kuma bayar da magani ne ba ruruta cuta ba.
4, Ya inganta a Hadisi Manzon Allah SallalLahu AlaiHi wa AliHi wa sallam Ya la’anci duk mai shan giya (Alla’anul mudlaq)
Ya inganta a Hadisi Manzon Allah SallalLahu AlaiHi wa AliHi wa sallam Ya kwabi wanda ya la’anci wani mai shan giya (La’anul mu’ayyan).
5, Duk jarabawar duniya da ka shiga kada ka manta Allah Ta’ala Ya jarrabi waɗanda Ya fi so akanka da abinda ya fi wannan
Duk ni’imar duniya da ka samu kada ka manta Allah Ta’ala Ya baiwa waɗanda suka kafirce masa abinda ya fi wannan
Jarabawa da buɗin duniya ba ma’aunai bane na auna yarda da rashin yardar Allah Ta’ala.
Wadannan suke jawabai da Maulana Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari Hafizafullah babban limamin masallacin Abuja Nigeria. A wannan satin daya gabata a shafin sa na Facebook Page.
Muna addu’an Allah ya karawa rayuwar sa albarka, ya bada nasara a rayuwar sa. Allah ya kara lafiya da nisan kwana albarkacin Manzon Allah SAW. Amiin