Bikin Takutaha A Kano Ya Cika Shekaru 700 Da Fara Gudanarwa.

Bikin Takutaha A Kano ya cika Shekaru 700 biki ne na murnar yin nasarar rushe tsunburbura da yai dai dai da ranar Sunan manzon Allah Sallallahu Alaihiwasallam.

 

ASALIN BIKIN TAKUTAHA A KANO

 

TUN DAGA ZAMANIN SARKIN KANO ALI YAJI DAN TSAMIYA.

 

A duk 19 ga watan Rabiul Awwal, a jihar Kano kanawa suna gudanar da wani bikin Wanda ake Kira Takutaha.

 

Shin menene Asalin Tarihin sa ? Menene Alakar Bikin da Addinin musulunci ?

 

A wata shekara zamanin sarkin Kano Yaji dan Tsamiya, wasu malaman Wangarawa karkashin jagorancin sheikh AbdurRahman Zaiti suka zo, Kano, baya ga musulunci da kuma kasuwanci, suna da dabarun yaki da baa san da su ba a Kano. Bagaudawa suka karbi musulunci, hannun su, su kuma su taimaka musu don su yaki abokan gabarsu. Kwana daya da zuwansu Sarkin Kano Yaji ya karbi musulunci, ya kuma canjawa kansa suna zuwa Ali. Wanda hakan ke nuna, cewa , shirin yaki zaayi, domin ana cewa Ali bin Abu Talib shine sarkin yakin manzon Allah (saw). Kafin Ali yaji ya musulunta akwai musulmai a Kano saidai basu kai ga kafa mulki ba

 

A farkon watan Rabiul Awwal na wannan shekara, ne Yaji ya tara dukkan maguzawa, ya kuma karanta musu dokar-ta-baci. Inda yace musu

 

“Ku sani, daga yau, komai tsakanina daku, sai yaki da tsinin mashi, ba yaudara, bawani boye boye, domin ba mayaudari sai matsoraci, ku shirya gani nan zuwa gareku ko ku karɓi Addinin Musulunci kafin lokacin anyi masu wa’azi suka butulce”

 

Mataki biyu suka dauka, na farko sunyi kokarin bada cin hanci ga Sarki Yaji, amma yaki karba, yace a maida musu baya so. Na biyu, sai suka koma ga Tsumburbura, domin neman nasara, amma ta gaya musu, cewa wannan yaki ba nasara, domin lokacin karshen addininsu a kasar Kano yazo.

 

Acikin watan dai, rundunar musulmi suka fuskanci, rundunar maguzawa, a gefen Dutsen Dala, inda suka hadu, aka gwabza. A wannan lokacin ne, Jarmai Bajere ya samu nasarar Kutsa kai cikin shigifar Tsumburbura, inda ya samu wani halitta na tsaye, rike da maciji a hannunsa, ya daga mashi ya bugawa halittar nan, tayi kuwwa ta fito a guje. Nan da nan suka bita, inda ta nufi kofar ruwa, ta fada cikin ruwan Dankwai. Wannan Shi ya kawo karshen Tsumburbura, da kuma addinin maguzawa a garin Kano.

 

Samuwar wannan Nasara, ba karamin abu bane a wurin musulman Kano. Wanda aka shafe sama da shekaru 100 ana nema. A dalilin haka ne, ya sanya musulman kanawa duk shekara, sukan taru su hau Dutsen Dala domin tunawa da wannan nasara da musulunci yayi akan Maguzanci. Su nunawa duniya cewa, addinin Allah yau ya shafe addinin kafirai. Domin kafin zuwan musulunci, ba mai hawa Dala in ba Babban limamin addinin ba. Amma zuwan musulunci, yanzu kowa ma sai ya hau, ya yi kashi ma aka. Wannan shine dalilin da ya sanya ake takutaha a duk shekara a Kano.

 

MENENE MA’ANAR KALMAR TAKUTAHA ?

 

An sha kai-kawo a tsakanin masana game da ma’ana ko asalin wannan kalma ta takutaha. Wannan ce ta sa aka sami mabambantan ra’ayoyi game da wannan kalma.

 

Daga ciki akwai Hassan (1998:94) ya nuna cewa, bayan al’ummar Kano sun rungumi wannan rana ne ta takutaha, sai Maguzawa da suke gabatar da bukukuwansu na bauta a lokacin suka damu, wasu suka bar garin zuwa qauyuka, suna cewa, “wannan sallar taku-ta ba tamu ba ce”. Daga nan sai aka sami kalmar takutaha.

 

Wasu kuwa suna ganin Kalmar ta samu ne daga qaulin Shehu Usmanu Danfodiyo, a lokacin da almajiransa suka yiyo bara a ranar da shekarar da aka haifi Annabi salallahu alaihi wasallam ta kewayo, amma sai ya qi daukar komai a ciki, ya ce, “ ai wannan taku ta”. Daga nan sai aka sami kalmar “takutaha”.

 

Wasu kuma suna ganin ma’anar Kalmar takutaha ita ce, “Allah ya maimaita mana”, wasu kuma sun ce sunan Ma’aiki ne. Haka nan, wasu suna ganin Kalmar ta samu ne daga sunan wata baiwar Allah mai suna Taku, ‘yar Malam Usman Attuman, babban waliyin nan da ya zauna a Madabo.

 

A dunqule, za a iya cewa bikin takutaha yana daya daga cikin bukukuwan addini da ake yin sa a birnin Kano, duk ranar 19 ga watan Rabi’ul awwal, wato watan da aka haifi Annabi Muhammadu salallahu alaihi wasallam kuma dai-dai da ranar sunan sa.

Share

Back to top button